August 3, 2021

  Tasirin Azabtarwa Akan Halayyar Ammar

Daga Mallam Mujtaba Adam

Cigaba daga inda muka tsaya…

Tarihin rayuwar Ammar na musamman  ne,wanda ya ke cike da izina ga wanda ya ke son daukar darasi. Za mu iya daukarsa a matsayin kyayyawan misali na mutumin da ya rayu a kaskance sannan ya yi gwagwarmaya mai tsawo ya hau matakalan kaiwa ga matsayin da ya kere na wadanda su ke yi masa kallon wulakanci. ( kuraishawa bangaren Umayyawa na jahliyya da kuma munafikansu da  Musulunci ya ci su da yaki.)

Wani abu da ya dace a yi ishara da shi anan shi ne cewa,  a lokacin da Ammar ya musulunta ya fuskanci ukuba da azabtarwa daga Kuraishawa da wani mahaluki bai fuskanci irinta ba. Ammar ya shahara ne saboda azabtarwar da Kuraishawa su ka yi masa. Labarin yadda aka azabtar da shi, yana a matsayin  kyakkyawan misali ne na irin tursasawar da Kuraishawa su ke yi wa mabiya sabon addini. Ammar,  ya kebanta da cewa ana azabtar da shi shi da danginsa a lokaci guda. Wannan azabtarwar ce ta yi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa da mahaifinsa. An kuma jefo da dan’uwansa daga kan katanga ya mutu akan tafarkin Musulunci. Tabon azabtarwa bai rabu da fatar jikin Ammar ba har zuwa karshen rayuwarsa.

Muhammad Ibn Ka’ab al-Qardhy ya bada labarin cewa: “ Wata rana ya ga gadon bayan Ammar da ya ke a bude. Sai ya ga tabon rauni ajikinsa. Da ya tambaye shi sai Ammar ya fada masa cewa: Wannan alamun azabtarwar da Kuraishawa su ka rika yi mani ne akan rairayin Makka mai kuna.” ( Littafin Abdullah al-Subaiti da ya gabata.)

Ga dukkan alamu, wannan mummunar azabtarwar ta haifar da kwantacciyar kiyayya ga Kuraishawa a cikin boyayyen hankalin Ammar. Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne a wannan rayuwar ta duniya,  a ce an azabtar da wani mutum irin azabar da aka gasawa Ammar,  a kuma kashe mahaifinsa,  da mahaifiyarsa da kuma dan’uwansa  ta hanyar azabtarwa  sannan kuma a ce ya mance.- Sai dai idan jaki ne ba mutum ba.

Abu ne mai yiyuwa a ce wannan  kwantacciyar kiyayyar ta yi tasiri a cikin halinsa. Watakila  kuma tasirin hakan ya karu, a lokacin da ya ga mutanen da a baya suka azabtar da shi, an wayi gari sun sake samun aiko a lokacin Usman. Watakila a wannan lokacin ya tunano da mawuyacin halin da ya shiga a lokacin da aka kashe mahaifinsa da mahaifiyarsa da kuma dan’uwansa ta hanyar a zabtarwa akan rairayin Makka.

Aduk lokacin da  Ammar ya ga wani Bakuraishe mai jan wuya a gabansa yana saurin zaginsa. Su kuwa Kuraihsawa masu jan wuya suna shayinsa saboda matsayinsa a wurin annabi, sannan kuma da wurin Abubakar da Umar daga baya. Bisa karamin dalili Ammar yana zaginsu su kuwa su kyale shi.

 

An ambaci cewa wani lokaci ya zagi Khalid Bin Walid,  sai Khalid din ya je waurin annabi ya fada masa cewa: “ Ya manzon Allah ya kyale wannan bawan yana zagina? Wallahi ba domin kai ba da bai zage ni ba.” (Littafin da ya gabata na Abdullahi al-Subaiti)

Wata rana kuma ya zagi Amru Bin As. Sai Amru ya maida masa jawabi na makirci a gaban mutane da cewa: “ Ka zage ni alhali ni ban zage ka ba.”

Ya kuma zagi Abbas Ibn Abi Lahab a wani wuri. (al-Awasin Minal Qawasim: Ibn Arabi.)

A lokacin shawarar zabar Usman, Ammar ya dauki matsayi mai tsanani. Baya son a zabi Usman, Ali Ibn Abi Talib  ya ke so a zaba. Kai kace yana daukar Usman a matsayin mai wakiltar Kuraishawa.

Lokacin da aka zabi Usman, Ammar ya ji zafi sosai ya mike a cikin masallaci yana fada. Ya kuma ci gaba da nunawa Usman adawa har zuwa karshe. (al-Fitnatul-Kubrah: Taha Hussain.)

 

zamu cigba…

SHARE:
Makala 0 Replies to “  Tasirin Azabtarwa Akan Halayyar Ammar”