November 23, 2021

Tashar Arewa24 zata fara watsa shirye-shiryen tashar Aljazeera cikin harshen hausa

Daga Balarabe Idriss


Tashar labarai ta Aljazeera da kuma tashar Arewa24 sun cimma matsaya kana kuma sun bayyana cewa sun kammala shirinsu na fara fassara shirye-shiryen da ake gudanarwa a tasahar labaran Aljazeera izuwa harshen hausa don al’ummar arewacin Nijeriya.

Yarjejjeniyar na nufin cewa za’a rika fassara shirye-shiryen tashar Aljazeera zuwa harshen hausa kana kuma a sanya su a tashar Arewa24 wacce ke da masu kallo sama da mutane miliyan 40 daga sassan arewacin Nijeriya, Nijar, Chadi da kuma Kamaru.

Shirye-shiryen kuwa zasu rika zuwa ga masu kallo daga tashar ta Arewa24 ta hanyoyin da suka hada da DStv, StarTimes, CANAL +, TSTV da kuma manhajar “AREWA24 on Demand”
Zabbaben shugaba na tashar ta Aljazeera; Ramzan Alnoimi ya bayyana cewa sun yi matukar farin ciki da wannan hadin gwiwar, kamar yadda ya nuna cewa hakan na nufin shirye-shiryen tashar su zai rika riskar miliyoyin sabbin jama’a a sassa da dama na nahiyar Afirka a bisa yaren da suke fahimta.

A bangare guda kuwa, mamallakin tashar Arewa24; Jacob Arback ya bayyana farin cikin sa maras misaaltuwa kan wannan yarjejjeniyar, inda ya ce dole su yi farin ciki na kasancewa tasha ta farko da zata fara watsa shirye-shiryen Aljazeera kuma a harshen hausa wacce ta kasance yaren da mutane sama da miliyan 90 ke fahimta a yammacin Afirka.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Tashar Arewa24 zata fara watsa shirye-shiryen tashar Aljazeera cikin harshen hausa”