January 16, 2023

Tarwatsewar Gurneti Ta Yi Sanadiyyar Halakar Sojan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Tarwatsewar gurneti ya yi sanadiyyar halakar sojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Israila guda tare da jikkatan wasu na daban

Majiyar rundunar sojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta fitar da sanarwar cewa: Wani sojan Isra’ila ya sheka lahira, yayin da wasu hudu na daban suka samu munanan raunuka, sakamakon fashewar gurneti a wani sansanin soji.

Binciken farko-farko da rundunar sojin ta gudanar yana nuni da cewa: Sojan da ya halaka ya sanya gurneti a cikin jakarsa ce a lokacin atisayen soji, sannan ya dauki jakar zuwa dakin kwanan sojojin da ke cikin sansanin, inda fashewar gurnetin ya yi sanadiyyar halakarsa da jikkata wasu sojoji hudu na daban.

Wannan lamari shi ne irinsa na biyu a cikin mako guda, inda wani abu ya fashe a yammacin ranar Litinin da ta gabata a wani sansanin sojin Haramtacciyar kasar Isra’ila da ke Lardin Jenin a arewacin gabar yammacin kogin Jordan.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Tarwatsewar Gurneti Ta Yi Sanadiyyar Halakar Sojan Haramtacciyar Kasar Isra’ila”