TARIHIN SHI’A DA A’KIDOJIN TA KASHI NA (15)

Dorawa daga Kashi na (14) da yagabata:
2-Ta wannan hanya kuma ya rubuta cewa: [Sarriyu ya rubuta zuwa gare ni, daga Shu’aibu daga Saif daga Muhammad bin Auf, daga Ikrama, daga Ibin Abbas ya ce: “Abu Zarri ya kasance yana kai-komo tsakanin al-Rabza da Madina saboda tsoron Larabawan kauye (kar su yi ridda). Ya kasance yana son kadaita da Halwa. Sai wata rana ya shiga wajen Usman, a tare da shi – Usman – akwai Ka’abul-Ahbar, sai ya cewa Usman: ‘Kar ka shagwaba mutane da rashin yi musu hukunci har sai sun rika kyautatawa! ya kamata ne wanda ya fitar da Zakka kada ya takaita da ita har sai ya kyautawa makota da ’yan’uwa, kuma ya sadar da zumunci (ta hanyar taimako).’ Sai Ka’abu ya ce: ‘wanda ya sauke farilla ai ya sauke abin da ya hau kansa.’ Sai Abu Zarri ya daga sandarsa ya dake shi da ita sai da ya ji masa ciwo!’ sai Usman ya lallabe shi da cewa ya kyautar masa da sandar, sai ya ba shi, sannan sai – Usman – ya ce: ‘ya kai Abu Zarri, ka ji tsoron Allah! ka kame hannun ka da harshen ka daga cutar da mutane!’ da ma kafin nan ya cewa Ka’abul-Ahbar: ‘kai dan Bayahudiya! me ya hada ka da abin da kenan wajen? wallahi ko dai ka saurare ni ko in yi maganin ka!!’] (duba: Tarikh al-Umam Wal-Muluk na Ibin Jarir at-Tabary, juz’i na 1, lamba na 2860 -2861).
3-Ya ruwaito wannan tastuniya ta wata fuska da cewa: [Sarriyu ya rubuta zuwa gare ni, daga Shu’aibu, daga Saif, daga Asha’athu bin Siwaar, daga Muhammad bin Siriina ya ce: “Abu Zarri ya fita zuwa al-Ribzah a kashin kansa, a lokacin da ya ga Usman bai yi sha’awar ra’ayinsa ba, kuma Mu’awuya ya fitar da mutan-gidansa (daga Sham) a bayansa; sai suka fita zuwa gare shi rike da wata jaka (ta fata), wadda ke nauyaya hannun namiji (wanda yake dauke da ita); sai ya ce: ‘dubi abin da ke wajen wanda yake gudun duniya!’ Sai matarsa ta ce: ‘wallahi babu Dinari ko Azurfa a ciki sai dai sulalla ne; ya kasance idan tallafin da yake samu daga hukuma ya ishe shi ya kan sayi sulalla don biyan bukatun mu’. Lokacin da Abu Zarri ya sauka, sai aka tayar da Sallah karkashin wani mutum mabaraci, sai (wannan mutum) ya ce: ‘bisimilla, ka ja mu Sallah ya Aba Zarri;’ sai Abu Zarri ya ce: ‘a’a, ka ja mu Sallah, domin Manzon Allah (Sallallahu Aalaihi Wa’Aalihi) ya fada min cewa: {ka saurara kuma ka yi biyayya ko da wanda yake jagorancin ka bawa ne mai gundulmi}, kai kuwa (duk da) bawa ne (amma) ba mai gundulmi ba ne’; (mutumin ya kasance cikin bayin sadaka, ya kasance bawa, ana kiransa Mushaji’u] (duba: Tarikh al-Umam Wal-Muluk na Ibin Jarir al-Tabary, juz’i na 1, lamba na 2861).
4-Haka ya ruwaito wannan tastuniya ta wata fuska da cewa: [Sarriyu ya rubuta zuwa gare ni, daga Mubasshir bin al-Fudail, daga Jabir ya ce: “Usman ya zartarwa da Abu Zarri babban lamari (hidima) a kowace rana, irin haka yayiwa Raafi’u bin Khudaij; su –biyun- sun kasance sun fice daga Madina saboda wani lamari da suka ji shi (amma) ba a fassara musu daidai ba, suka dauki ra’ayinsa kuma suka yi kuskure”] (duba: Tarikh al-Umam Wal-Muluk na Ibin Jarir al-Tabary, juz’i na 1, lamba na 2861).
Cigaba a kashi na (16)