August 16, 2023

TARIHIN SHI’A DA A’KIDOJIN TA KASHI NA (14)

 

Kafin mu kawo hukuncin malaman hadisi da masana halayyar maruwaita a kan Saif, yana da kyau mu ambaci yadda ambaton wannan kagaggen mutum ya zo a wasu wurare biyar a tarihin at-Tabari, bisa dogaro da isnadojin da suka kare da Saif dai. Ga su kamar haka:
Ya rubuta cewa:

1- [A wannan shekara (na talatin), abin da aka ambata dangane da al’amarin Abu Zarri da Mu’awuya ya faru; da yadda Mu’awuya ya mayar da shi Madina daga Sham. Hakika kuwa an ambaci dalilai masu yawa da suka sa ya koma da shi Madina daga Sham; wadanda na kyamaci mafi yawansu (dalilan). A wajen masu baiwa Mu’awuya uzuri a kan haka, sun ambaci wannan kissa kamar haka: Sarriyu ya rubuto min cewa, Shu’abu ya ba shi labari, daga Saif, daga Atiyya, daga Yazid al-Faq’asi ya ce: “lokacin da dan-bakar mace (shi ne lakabin da Saif yake kiran Abdullahi bin Saba’ din da ya kirkira da shi) ya zo Sham, sai ya hadu da Abu Zarri ya ce (da Abu Zarri): ‘Ya kai Abu Zarri, ba ka mamakin Mu’awuya kan yadda ya ke kiran dukiya (wadda take baitul-mali) da cewa dukiyar Allah ce? kamar dai yana son ya danne ta ne koma bayan Musulmi!’

SAI Abu Zarri ya tafi gare shi (Mu’awuya din) ya ce: ‘Me ya sa kake kiran dukiyar Musulmi da sunan dukiyar Allah?’ sai –Mu’awuya – ya ce: ‘Allah Ya huci zuciyar ka Ya Aba Zarri, shin mu ba bayin Allah ba ne? Alhali dukiyar kuma ta Shi ce, kuma (ai) halittu (duk) halittarSa ce kuma (dukkan) lamari na Shi ne!!’ Sai –Abu Zarri- ya ce: ‘to kada ka rika fadin haka (cewa dukiya ta Allah ce)’. Sai – Mu’awuya – ya ce: ba zan sake fadin cewa ta Allah ba ce, amma zan rika cewa dukiyar Musulmi ce’.” Sai – mai ruwaya – ya ci gaba de cewa: “haka nan dan bakar-macen ya tafi wajen Abu Darda’i, sai – Abu Darda’i – ya ce da shi: ‘kai wanene? wallahi ina tsammanin – kai – Bayahude ne!’’ Sai ya tafi wajen Ubadata bin Samit, ya makale a wajensa. Sai –wata rana – ya tafi da shi wajen Mu’awuya ya ce: ‘wallahi wannan ne yake zuga Abu Zarri a kan ka!” Sai Abu Zarri ya rika yawo a Sham yana cewa: ‘ya ku mawadata! ku tausayawa matalauta –Allah Madaukaki Yana cewa – {Kuma ka yi albishir ga wadanda suke boye zinari da azurfa, kuma ba sa ciyar da ita a tafarkin Allah, da azaba mai radadi. A ranar da za a kona su a kanta (dukiyar) a cikin wutar jahannama….} al-Taubah/35.’

Bai gushe ba yana aikata haka har sai da talakawa suka rudu da irin kiransa, suka tilasta haka a kan mawadata, har sai da mawadatan suka fara kokawa da abin da suke fuskanta daga talakawa. Sai Mu’awuya ya rubutawa (Khalifa na uku) Usman cewa: ‘lallai Abu Zarri ya matsa min! yana aikata kaza da kaza!!’ Sai Usman ya aika masa da cewa: ‘Hakika fitina ta fara kunno kai! babu abin da ya saura sai a dakatar da kunnuwarta, ta yadda ba za ta zama matsala ba! don haka ka shirya Abu Zarri ka aiko min da shi tare da dan ja-gora; kuma ka ba shi guzuri, sannan ka bi shi a hankali; ka kare kanka da mutane gwargwadon iko; ka ci gaba da riko da abin yake karkashin ka (na mulki). Sai (Mu’awuya) ya aika da Abu Zarri da wani ja-gora a tare da shi. Lokacin da ya isa Madina ya ga gine-ginen jama’a sun kai tsawon dutsen Sil’u (wani dutse ne a Madina kusa da Masallacin Manzon Allah Sallallahu Aalaihi Wa’Aalihi), sai ya ce: ‘ka yiwa mutanen Madina albishir da wani samame wanda ba ya kyale kowa tare da masifaffen yaki’.

Sai ya shiga wajen Usman, sai – Usman din – ya ce: ‘Me ya sa mutanen Sham suke kuka da abin da ke fitowa daga bakin ka?’ Sai ya ba shi labari da cewa bai kamata ana alamta dukiyar baitul-mali da dukiyar Allah ba, kuma bai kamata mawadata su rika boye dukiya ba. Sai – Usman – ya ce: ‘ya kai Abu Zarri, abin da nake yi kawai shi ne sauke nauyin da ya hau kaina na karbar abin da ya zama dole a wuyan wadanda nake shugabanci, ba zan tilasta su a kan zuhudu (gudun duniya) ba, ko in kira su zuwa kokarin tattali ba’. Sai –Abu Zarri – ya ce: ‘To ka ba ni izni in fice – daga Madina – saboda Madina ba wurin zama ba ne gare ni’.

Sai – Usman – ya ce: shin akwai wani wuri da za ka musanya da garin Madina – face wanda ya fi shi sharri!.’ Sai – Abu Zarri – ya ce: ‘Manzon Allah (Sallallahu Aalaihi Wa’Aalihi) ya umarce ni da cewa in fita daga Madina a duk lokacin da tsawon gine-ginenta ya kai dutsen Sil’u’. Sai – Usman – ya ce: ‘to ka aiwatar da abin da (Manzo) ya hore ka da aikatawa’”. Sai –mai ruwaya- ya ce: “sai kuwa ya fita har sai da ya kai al-Rabza (wani sarari ne dake nesa da Madina da nisan tafiyar kwana uku). Abu Zarri ya zauna a wajen daga shi sai matarsa da dansa har zuwa karshen rayuwarsa): ya gina Masallaci, kuma Usman ya ba shi wani adadi na rakuma (a wani tarihin har da garken tumaki amma at-Tabri bai ambaci wannan ba), ya kuma ba shi bayi guda biyu; ya kuma aika masa da cewa: ‘ka rika zuwa Madina a kai a kai ta yadda wani Balaraben kauye ba zai yi ridda ba’, sai kuwa ya aikata haka”] (duba: Tarikh al-Umam Wal-Muluk na Ibin Jarir al-Tabary, juz’i na 1, lamba na 2858 -2860, wajen ambaton abubuwan da suka faru a shekara ta 30 bayan hijra).
Cigaba a kashi na (15)

SHARE:
Raruwar Magabata, Shubuhohi Da Raddodin Su 0 Replies to “TARIHIN SHI’A DA A’KIDOJIN TA KASHI NA (14)”