August 22, 2021

Tarihin Sayyid Khamenei (DZ)

HAIHUWARSA DA NASABARSA

An haifi Ayatullahi Alhaj sidi Ali Alhusaini Khamina’i (Allah ya ja kwanansa) a shekarar (1939m) a garin Mashhad, cikin zuriya ta ilimi abar girmamawa.

Sunan mahaifinsa: Alhaj sidi Jawad, wanda ya kasance babban malami a garin Mashhad kuma daya ne daga cikin mujtahidai, shi ne limami a Kohrshad a masallacn Bazar a garin na Mashhad, ya kuma kasance daya daga cikin fitattun muballigai. Ya rasu a watan Zulqi’ida ta shekarar (1407H) yana dan shekara casa’in da uku (93).

Sunan kakansa Ayatullahi sidi Alhusaini Alkhamina’i, shi kuma ya kasance daya ne daga cikin malaman Azarbajan, ya rayu a qauyen Khayaban a Tabriz, daga nan ya yi hijira zuwa Najaf ya zauna a can, ya rinqa koyarwa kuma yana yin bincike na ilimi. Ya kasance mai ilimi da kuma tsoron Allah madaukakin sarki, ya gudanar da rayuwarsa cikin zuhudu tare da yarda da abin da Allah ya ba shi.

Mahaifiyarsa ‘ya ce ga hujjatul Islam sidi Hashim Najaf Abadi, wanda ya kasance daya ne daga cikin malaman Mashhad, ta kasance madaukakiya, mai ilimin mas’alolin addini da Akhlaq, ta rasu a watan Muharram a shekara ta (1409H) tana ‘yar shekara (76), sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

Ta bangaren zamantakewar iyali kuwa, sidi Khamina’i yana da aure, kuma yana da ‘ya’ya shida.

QURUCIYARSA:

Ayatullahi sidi Khamina’i ya rayu lokaci mai tsawo a qarqashin kulawar mahaifinsa wanda ya kasance mai tsananin sanya ido wajen tarbiyyantar da ‘ya’yansa tare da ilmantar da su. Ya kasance mai tausasawa da nuna qauna a gare su, kamar yadda mahaifiyarsu ta kasance tana nuna musu fiye da na mahaifin nasu.

Sun rayu a cikin qunci na qarancin abin hannu, kamar yadda ya kasance yana fadi: “Haqiqa na yi quruciyata cikin qunci mai tsanani, musamman da ya kasance lokaci ne ne yaqi, duk da cewa garin Mashhad ba ya cikin wuraren da yaqin ya rutsa da su, kuma akwai kayayyakin bukata da sauqin farashi fiye ma da sauran garuruwan, ta yadda har ba ma iya cin gurasar alkama, mun fi cin gurasar sha’ir, a wani lokacin kuma mukan samu ta sha’ir din da kuma ta alkama, sai dai ba mu cika samun hakan ba.

 

Imam Khamenei a lokacin kuruciya

Ina iya tuna cewa a lokacin quruciyata a wasu lokutan ba ma iya samun abincin dare, wasu lokutan kuma mahaifiyata takan karvi kudin da kakata ta ba ni ko kuma ta ba wa daya daga cikin ‘yan uwana domin ta saya mana madara ko zabib don mu ci gurasa da shi. Sannan fadin gidan da aka haife nu bai wuce mita (60-70) ba a cikin unguwar talakawa a Mashhad.

A gidan akwai wani dakin qarqashin qasa wanda idan aka yi baqi muke shiga cikinsa, kasantuwar mahaifina malami kuma marji’i, sai ya kasance yana yawan yin baqi, don haka mu kuma sai mu shiga wannan dakin mu bar musu wurin har sai sun tafi.

Bayan wani lokaci sai wani daga cikin almajiran mahaifina ya saya masa wani kango da yake jikin gidanmu, sai aka shigar da shi gidan namu, ya qara fadi ya zama gida mai dakuna uku.

Tufafin da muke sanyawa kuwa mahaifiyarmu ce take dinka mana kaya daga tsofaffin tufafin mahaifina, ya kasance yana dadewa bai canza kaya ba, ga misali daga cikin tufafinsa akwai wanda ya shekara arba’in bai canza shi ba”.

A biyo mu don cigaba…

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Tarihin Sayyid Khamenei (DZ)”