September 2, 2021

TARIHIN MAKOKIN IMAM HUSAINI (A.S)

Mallam Mujtaba Shuaibu Adam

Makokin juyayin shahadar imam Husaini (a.s) a tarihi yana da fuskoki guda biyu:

  • Kafin aukuwar ta’addancin a aikace.
  • Bayan aukuwar ta’addancin.

Koka wa imam Husaini (a.s) kafin aukuwar ta’addancin a aikace yana nufin tausayawa da yin Allah wadai tare da la’antar da annabawan Allah da mala’iku suka yi sakamakon sanar da su labarin aukuwar lamarin da Allah madaukakin sarki ya yi.

Daga cikin annabawan da suka koka wa manzon Allah (s.a.w) game da kisan imam Husaini tare da sauran ‘yayan manzon Allah (s.a.w) akwai:

1 – Annabi Adam (a.s): Ya zo a cikin littafin: Durru Assamin, lokacin da yake yin tafsirin wannan aya:

(فتلقى آدم من ربه كلمات فتاب عليه إنه هو التواب الرحيم)[1].

Ma’ana: Sai Adamu ya fuskanci Ubangijinsa da wasu kalmomisai sai  ya gafarta masa, lallai Ubangiji mai gafara ne kuma mai rahama.

Sai mai littafin ya ruwaito cewa: Annabi Adam (a.s) ya ga sunan annabi Muhammad da imamai a cikin Al’arshi, sai mala’ika Jibrilu ya laqqana masa ya ce:

(يا حميد بحق محمد، يا عالي بحق علي، يا فاطر بحق فاطمة، يا حسن بحق الحسن والحسين ومنك الإحسان).

Ma’ana: Ya abin godiya don alfarmar Muhammad, ya madaukaki don alfarmar Ali, ya wanda ya qagi halitta don alfarmar Fatima, ya wanda yake shi ne kyawu don alfarmar Hasan da Husaini dukkan kyautatawa tana gare ka.

Lokacin da ya ambaci Husaini sai hawaye ya zubo masa, ya kuma ji zuciyarsa ta karye. Sai ya ce: Ya dan uwana Jibrilu, me ya faru lokacin da na ambaci mutum na biyar sai na ji zuciyata ta karye, hawaye ya rinqa zubowa daga idanuwana?

Sai mala’ika Jibrilu ya ce da shi: Wannan dan naka zai hadu da masifar da dukkan masifu za su zama qanana a tare da ita.

Sai annabi Adam ya ce: Wace irin masifa ce wannan?

Sai ya ce: Za a kashe shi yana mai tsananin qishi, shi kadai ba shi da wanda zai taimaka masa. Zai rinqa kukan qishi da rashin mataimaki, har sai qishin ya sa ya rinqa ganin duniyar tamkar hayaqi, babu wanda zai amsa masa sai dai ya ji saukar takubba tare da shayar da shi nau’o’in mutuwa, za kuma a yanka shi tamkar yadda ake yanka rago, sannan maqiyansa su wawashe kayansa da matansa, za kuma a rinqa zagayawa da kawukansu shi da mataimakansa a cikin garuruwa tare da matansu, lallai haka abin zai kasance a ilimin Allah. Sai annabi Adamu da mala’ika Jibrilu suka fashe da kuka mai tsanani.

Haka kuma, Allama majlisi ya sake ruwaito cewa: lokacin da Allah madaukakin sarki ya sauko da annabi Adamu zuwa doron qasa bai ga Hauwa’u ba, sai ya yi ta zagayawa a duniya yana neman inda take, har ya biyo ta Karbala, sai ya ji baqin ciki ya turnuqe shi ya fadi a wurin da aka kashe imam Husaini (a.s) yana zubar da hawaye. Sai ya tambayi Allah madaukakin sarki da cewa: Ya Allah ko na sake aikata wani zunubi ne daban ka ladabtar da ni saboda shi? Domin na kewaya ko’ina a duniya babu abin da ya same ni sai a nan wurin.

Sai Allah ta’ala ya yi masa wahayi da cewa: Ya Adamu babu wani laifi da ka aikata, sai dai a wannan wurin ne za a kashe danka Husaini yana abin zalunta, don haka ne jininka ya zuba a wurin saboda dacewar da ke tsakaninku.

Sai annabi Adamu ya ce: Shin Husaini shi ma Annabi ne?

Sai Allah madaukakin sarki ya ce: A’a, sai dai shi jikan annabi Muhammadu ne.

Sai annabi Adamu ya ce: Wane ne zai kashe shi?

Sai Allah madaukakin sarki ya ce: Wanda zai kashe shi shi ne: La’anannen sammai da qassai.

Sai annabi Adamu ya ce da Jibrilu: Me zan in aikata?

Sai Allah ya ce: Ka la’ance shi ya Adamu.

Sai annabi Adamu ya la’ance shi har sau hudu, daga nan ya ci gaba da tafiya zuwa dutsen Arafa sai ya iske Hauwa’u a can.

2 – Annabi Nuhu: Shi ma ya la’anci makasan imam Husaini da wadanda suka tozartar da shi.

Allahma Majlisi ya ce: An ruwaito cewa lokacin da annabi Nuhu suka hau jirgin ruwa ya yi ta zagayawa da su a cikin duniya, lokacin da suka zo Karbala sai qasa ta kama jirgin nasu, har sai da annabi Nuhu ya ji tsoron nutsewa.

Sai ya roqi Allah madaukakin sarki cewa: Ya Ubangiji! Mun zagaya ko’ina a cikin duniya wani abu irin wannan bai same mu ba sai a wannan wurin.

Sai mala’ika Jibrilu ya sauka ya ce: Ya Nuhu, a wannan wurin ne za a kashe Husaini jikan cikamakin annabawa, kuma cikamakin wasiyyai.

Sai annabi Nuhu ya tambayi mala’ika Jibrilu cewa: Wane ne zai kashe shi?

Sai ya ce: Wanda zai kashe shi shi ne la’anannen sammai bakwai da qassai bakwai.

Sai annabi Nuhu ya la’ance shi har sau hudu, daga nan sai jirgin nasu ya ci gaba da tafiya har ya kai wani wuri da ake karansa Judi ya tsaya a kai.

3 – Annabi Ibrahim Badadin Allah: An ruwaito daga imam Rida (a.s) cewa: Lokacin da Allah madaukakin sarki ya umarci annabi Ibrahim ya yanka rago a madadin dansa Isma’il, ya so a ce ya yanka dan nasa da hannunsa don ya samu mafi daukakan ladan wadanda suke juriya ga masifu.

Sai Allah ya yi masa wahayi da cewa: Ya Ibrahim, wa ka fi so a cikin halittata?

Sai annabi Ibrahim ya ce: Ai ba ka taba halittar da na fi so fiye da masoyinka Annabi Muhammad ba.

Sai Allah ya ce da shi: Shi da kanka wa ka fi so?

Sai annabi Ibrahim ya ce: Na fi sonsa fiye da kaina.

Sai Allah ya ce: Da dansa da naka wanne ka fi so?

Sai ya ce: Na fi son dansa.

Sai Allah ya ce: Da a ce azzalumai su yanka dansa yana abin zalunta da kuma ka yanka danka da hannunka a cikin da’ata wanne ne ya bugun zuciyarka.

Sai annabi Ibrahim ya ce: Yanka dansa yana abin zalunta shi ne ya fi bugun zuciyata.

Sai Allah madaikakin sarki ya ce: Ya Ibrahim, lallai wasu jama’a da suke raya cewa su ma suna cikin al’ummar Muhammad za su kashe Husaini a bayansa bisa zalunci da wuce gona da iri, za su yanka shi kamar yadda ake yanka rago, da wannan za su wajabta wa kawukansu fushina. Sai wannan magana ta bugi annabi Ibrahim ya rinqa yin kuka.

Sai Allah madaukakin sarki ya ce da annabi Ibrahim: Domin wannan damuwar da ka shiga da hawayen da ka zubar ga Husaini na karba maka abin da kake fatan samu da ka yanka danka Isma’il, kuma na wajabta maka samun mafificiyar daraja na ladan masu juriya ga masifa.

Da wannan ne Allah madaukakin sarki yake nufin fadinsa:

(وفديناه بذبح عظيم).[2]

A biyo mu a ruburu na gaba…

SHARE:
Makala 0 Replies to “TARIHIN MAKOKIN IMAM HUSAINI (A.S)”