January 3, 2023

TARABA: Yan Bindiga Sun Kashe Akalla Mutum Biyar Sun Kuma Kona Rugage Da Dama

Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun kashe mutane fiye da biyar sun kuma kona rugage sama da goma sha daya a kauyen Ngura dake a karamar hukamar Yorroo na jihar Taraba.

Ardo Ummar Bello da ke zama Ardon Ngura wanda lamarin ya faru a idonsa ya shidawa Muryar Amurka cewa ‘yan bindigan sun zo ne da manya manyan makamai su ka fara kashe kashe da kone kone har su ka kona gidaje akalla sha biyar da kuma kashe mutane fiye da biyar. Haka zalika suka kona kayan anfanin gona a harin.

Shi kuwa Hassan Abdullah, mahaifinsa ne aka kashe a wannan hari inda suka kuma gudu da gawarsa. Ya ce suna cikin halin tashin hankali na rashi samun gawar mahaifin nasa domin a yi masa jana’iza.

Alhaji Abdu daya daga cikin wanda lamarin ya faru a idonsa, cewa ya yi suna cikin mawuyachin hali wanda basu taba ganin irinsa tun da suke duniya kuma sun yi kokari sanar da hukumomi na jihar Taraba, amma kawo yanzu dai shiru ka ke ji ba wani labari domin ganin an kamo masu hannu cikin wannan harin.

Sai dai a yayin hada wanna rahoton duk kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandar jihar Taraba ya ci tura.

©VOA

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “TARABA: Yan Bindiga Sun Kashe Akalla Mutum Biyar Sun Kuma Kona Rugage Da Dama”