August 22, 2021

TARABA: Miyetti Allah Ta Mika Masu Garkuwa Da Mutane Ga Hukumar ‘Yan Sanda

Muhmammad Bakir Muhammad

A ranar Lahadin 22 ga wata Agusta ne jungiyar Miyetti Allah ta jihar Taraba ta mika wasu musa garkuwa da mutane da masu sana’ar sayar da bindiga wanda adadin su yakai 11 ga hukumar ‘yan sandar jihar ta Taraba, shugaban Kungiyar Miyetti Allah na jihar Taraba Malam Sahabi Tukur yace wannan dai sakamako ne na alkawarin da suka yi ma  Sarkin Muri da kuma hukumar ‘yan sanda kan cewa zasu yi iya bakin kokarin su wurin zakulo masu laifuka dake tsakanin su. Ya kuma kara da cewa sun nada wakilai cikin dukkanin bangarorin da suke da shin a Fulani domin yin aikin tare da ‘yan sanda da kuma sauran hukumomin tsaro a dukkanin kananan hukumomi 16 da suke jihar domin zakulo masu garkuwa da mutane da sauran masu manyan laifuka.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar yayi kira ga fulanin jihar don taimakawa wurin kama bata gari dake tsakaninsu.

Ya kuma kara da cewa akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin jahohin Benuwai, Adamawa da kuma Taraba don shawo kan matsalar ta garkuwa da mutane a yankin.

Kwamishinan ya kuma tabbatar da goyon bayan ‘yan sanda ga Fulanin wurin kama bata gari da ke tsakanin su.

SHARE:
Tarbiyyan Yara 0 Replies to “TARABA: Miyetti Allah Ta Mika Masu Garkuwa Da Mutane Ga Hukumar ‘Yan Sanda”