November 21, 2021

Taraba: Mazauna iyakokin Kamaru da Nijeriya sun bayyana yadda jami’an shige da fice na Nijeriya suka hana yan awaren Ambazonia mamayar yankin

Daga Muhammad Bakir Muhammad


 

Mazauna garin Manga da ke jihar Taraba wacce ta ke kan iyakar Kamaru sun bayyana gagarumar jarumta da jami’an shige da fice na Imagireshon suka nuna yayin yunkurin dakarun yan awaren Ambazonia na mamayar yankin.

Kamar yadda rahotannin makon da ta gabata suka bayyana, yan awaren Ambazonia na kasar Kamaru sun kutsa kauyukan da ke jihar Taraba da nufin mamaya, inda suka kashe wani basarake da jama’ar sa, kana kuma suka kone gidaje da dama hade da makarantu.

A yayin da kwamitin binciken da aka nada kan binciken lamarin suka isa kauyen a jiya Asabat, mai magana da yawun mutanen kauyen; Abubakar Manga ya bayyana cewa mutane 13 ne suka rasa rayukan su a yayin yunkurin na yan awaren Ambazonia, mutane 13 kuwa sun hada da kananan yara 3, kana a bangare guda kuwa an rasa mutane akalla 20 wadanda har zuwa yau ba’a san inda suke ba.

Abubakar Manga ya bayyana cewa wani abu da ya sa lamarin bai munana sosai ba shine dauki da jami’an shige da fice suka kawo a yayin harin, ya kuma Kara da cewa ba don dauki da suka kawo ba da masu yunkurin sun shafe ilahirin kauyen.

Ya bayyana cewa dakarun na Ambazonia sun shigo kauyen be bayan ketare kogi kana kuma suka bi ta gefen tsaunuka da misalin 6 na safiyar Talata.

Abubakar manga ya ce dakarun sun fara ne da farmakar gidan sarkin garin kana kuma suka kashe shi.

Ya bayyana kuma cewa a wannan yanayin ne jami’an Imagireshon suka fuskance su, inda suka yi musayar wuta na tsahon lokaci Wanda ya tilastawa yan awaren Ambazonia guduwa da fita daga yankin.

Ya kuma Kara da cewa jami’an basu tsaya a iya haka ba, sun kuma yi nasarar ceto wasu mutane da suka fad’a kogi.

Daga karshe, Abubakar Manga ya kirayi gwamna Darius Ishaku da kuma hukumar soji da a kawo jami’an tsaro na musamman a yankin don kare mazauna yankin daga mamayar yan awaren.

Daga karshe kuma ya yi Kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya yi duba cikin lamarin, da kuma aikewa da jami’an tsaro a duk yankunan da suke iyaka da sauran kasashe don tabbatar da samuwar zaman lafiya.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Taraba: Mazauna iyakokin Kamaru da Nijeriya sun bayyana yadda jami’an shige da fice na Nijeriya suka hana yan awaren Ambazonia mamayar yankin”