November 18, 2021

Taraba: Kisan wani basarake ya haifar da hijira a kauyukan dake makobtaka da kasar Kamaru

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Daruruwan mutane mazauna kauyukan da ke makobtaka da kasar Kamaru a jihar Taraba sun kaurace wa daga gidajen su, hakan kuwa ya biyo bayan kisan mutane 11 wanda suka hada da wani mai sarautar gargajiya a yankin.
Kisan ya faru ne a yayin da sojojin awaren Ambazonia suka farmaki kauyukan, inda suka farmaki kauyukan da ke makobtaka da kasar ta Kamaru wadanda suke karkashin karamar hukumar Takum a jiya Laraba, kana kuma suka kashe mutane a kalla 11.

Sojojin na awaren Ambazonia sun kone gidaje da dama hade da makarantu kana kuma suka yi awon gaba da dukiyoyin al’umma.
Kantoman karamar hukumar ta Takum, Malam Shiban Tikari ya bayyana cewa sun gano gawarwakin mutane 5 daga cikin mutane 11 da aka hallaka, sai dai kuma ya zuwa yanzu babu labari kan sauran mutane 6 din.

Malam Tikari ya ce an zuba jami’ai na musamman cikin shirin ko-ta-kwana a yankin don kula da kauyukan da ke iyaka da kasar ta Kamaru.
An aiwatar da wannan matakin ne don jami’an su ba da tsaro ga lafiyar mazauna yankin da kuma kare su daga sojojin aware da kuma sojojin kasar ta Kamaru wadanda suka kasance suna yawan kai hari a kananan hukumomin Kurmi da Takum.
A watan da ya gabata ne sojojin kasar Kamaru suka kutsa kauyukan da ke iyakar Kamaru inda sukay barna tare da nuna cewa sun shiga yankin be don binciken yan awaren Ambazonia da ke boye a yankin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Taraba: Kisan wani basarake ya haifar da hijira a kauyukan dake makobtaka da kasar Kamaru”