January 3, 2023

Tankar Mai ta danne wani dan Achaba a Legas

Wani dan acaba ya makale biyo bayan faduwar tankar Mai mai dauke da lita 33,000 a kansa a kan titin Alaba Express dake babbar hanyar Apapa-Oshodi a jihar Legas.
A wata sanarwa da Daraktan hukumar kawo agajin gaggawa ta jihar Legas Malam Margaret Adeseye ya fitar a shafin tuwita, ya bayyana cewa matukin tankar ya rasa ikon kula da motar sabida jijjiga da take yi wanda ya haifar da faduwarta a gefen hanya har ta kai ga makalewar dan achaba din.
Jami’ai kawo agaji sun bayyana a wajen inda suke ta kokarin ceto rayuwar dan achaban da ya makale a karkashin tankar.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Tankar Mai ta danne wani dan Achaba a Legas”