July 21, 2023

Tambayoyi da Amsoshi akan zaman juyayin Abu Abdullahi a.s

T: An yi tambayar cewa mene ne ra’ayin Jagora dangane da gudanar da juyayin Ashura ba tare da riga ba? Idan har ba za a dauki juyayin a bidiyo sannan kuma babu mata a wajen fa? Shin a shar’ance yana ganin hakan a matsayin haramun ne?

Amsa: Yayin amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa Jagora ya kasance yana kiran wasu daga cikin mawakan juyayi da kada su dinga yin juyayin na su tsirara, wato ba riga a jikinsu. To amma hakan ba wai fatawa ce ta fikihu ba da za mu iya cewa haramun ne ba. To idan har babu wadanda ba muharramai ba a wajen, sannan kuma babu munanan abubuwa da ake yi, haka nan makiya ba za su yi mummunan amfani da hakan ba, mai yiyuwa ne mu ce ba haramun ba ne. A matsayin misali ‘yan wasu mutane ne suka taru, sannan kuma ba a dauka a bidiyo, haka nan kuma mazaje ne (ba mata a wajen), don haka sai suka cire rigunansu suna dukan kirjinsu. To amma a takaice kiran da yake yi – a matsayin kira da shawara – shi ne cewa kada mazaje su cire rigunansu yayin juyayin. Saboda me? Don mai yiyuwa ne akwai wadanda ba muharramansu ba a wajen don haka za su gansu, haka nan kuma mai yiyuwa ne makiya su yi amfani da hakan wajen yada bakar farfaganda a kan mazhabar Ahlulbaiti (a.s).

Tambaya: An yi tambayar cewa idan har mutum ya ta bugun fuskarsa a lokacin juyayin Ashura har ya ji wa fuskar rauni, shin akwai matsala cikin hakan?

Amsa: Yayin amsa wannan tambayar yana da kyau a fahimci cewa idan dai har kumburi da yin baki-baki ne, watakila saboda amfani da sarka, sannan kuma babu wata cutarwa ta asali ga jikin mutum, to a ra’ayin Jagora babu matsala cikin hakan. To amma duk wani abu sama da haka wanda mai yiyuwa ne makiya su yi mummunan amfani da shi, a matsayin misali mutum ya raunata kansa da jikinsa kamar masu amfani da wuka wajen saran jiki ko kansu (Tatbir), ko kuma shiga cikin wuta da makamantan hakan da wasu suke yi a wasu wajajen. To ala kulli hal dai wadannan ba wasu abubuwa ne da suke da asali cikin addini ba. Babu wani hadisi da yayi magana kansu sannan kuma tarihin Shi’anci bai ginu bisa hakan ba, kana kuma a halin yanzu makiya suna amfani da irin wadannan abubuwa wajen bakanta mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da mabiyansu. Idan har lamarin ya kai ga haka, to lalle akwai matsala. Amma idan har ya kasance kamar yadda aka saba ne, wato abubuwan da suka kumshi bugun kirji da bugun baya da sarka, mai yiyuwa ne jikin mutum ya yi ja da kuma kumbura, kamar dai yadda aka saba, ba tare da cutar da jiki ba, to hakan babu matsala cikinsa.

T: A wasu wajajen da ake tarurrukan juyayin, saboda yawan jama’a Husainiyoyi su kan cika ta yadda a kan rufe hanyoyin da suke gefe ko kuma hakan ya kan haifar da cinkoso da wahalar tafiya a kan hanyoyi. Shin akwai matsala cikin hakan? Ko kuma masu juyayin su kan daga muryoyinsu, shin akwai matsala cikin hakan idan har hakan ba ya cutar da mutane? Idan har akwai matsala, to ya ya batun halartar irin wadannan tarurruka kuma tare da cewa mutum ya san ba zai samu damar shiga cikin Husainiyar ba?

Amsa: Da farko dai juyayin shahadar Abi Abdillah al-Husain (a.s) yana daga cikin mafiya daukakar hanyoyin kusaci da Ubangiji. Yana da tasiri da albarkoki masu yawan gaske. A saboda haka wajibi ne a kiyaye hakan da kuma raya shi. Rayuwar Jagoran juyin juya halin Musuluncin cike take da misalan hakan ta yadda a wasu ranaku na shekara ya kan shirya irin wadannan tarurruka, inda zai zauna yana sauraren abubuwan da suka sami Imam Husain (a.s) daga bakin malamai. Amma a wasu ranakun, fitowa waje cikin tawaga-tawaga ta masu juyayin, irin su ranar Tasu’a da Ashura, suna daga cikin alamu na addini.

To a dabi’ance a irin wadannan lokuta za a rurrufe wasu hanyoyin, duk da cewa idan da za’a yi wani tsarin da zai sa ba za a rufe hanyoyin ba, shi ya fi. Amma yayin jerin gwanon irin su na Ranar Kudus da ranar 22 Bahman (ranar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran) da irin su Tasu’a da Ashura da makamantansu, a dabi’ance mafi yawan mutane su kan fito. To amma sabanin wadannan tarurruka, a samu wani yanayin da za a rufe hanyoyi, a wata Husainiya ko kuma wani mutum ya shirya taron juyayi a gidansa, ko da kuwa juyayin Shugaban shahidai (Imam Husaini) ne, ya saba wa dokokin gwamnati. Wato lalle akwai matsala cikin rufe hanyoyin mutane saboda taron juyayin da wani mutum ya shirya. Koda yake kamar yadda na ce Tasu’a da Ashura na su hisabin daban ne, don kuwa ana kirga fitowar irin wannan tawagar ta masu juyayi a matsayin wata alama ta addini. Don haka a dabi’ance za a rufe hanyoyi da dama, mutane ma suna da masaniya kan hakan saboda mafi yawa daga cikinsu da su ake yin wadannan tarurrukan. To amma sabanin wadannan tarurruka kan, yana da kyau muminai su kiyaye, kada su rufe wa mutane hanya, kada su daga muryoyin amsa kuwwarsu ta yadda za ta cutar da mutane, haka nan sautin kidan ganguna da sauransu da sauran ayyuka wadanda na gefe ne, irin su sansanoni da ake raba ruwa da shayi da sauransu fisabilillahi. Dukkanin wadannan abubuwa ne masu kyau amma kamata ya yi a yi su a wajajen da ba za su toshe hanyoyin mutane ba, haka nan kuma ba za su takura musu ba. Kamar yadda kuma yana da kyau a kiyaye tsaftar hanyoyin.

Dangane da tambayar da suka yi na cewa shin akwai matsala a halarci irin wadannan tarurrukan? A’a, babu matsala cikin halartar su ko da kuwa babu waje. Sai dai kawai kada a cutar da mutane da rufe musu hanya

SHARE:
Mas'alolin Fiqihu 0 Replies to “Tambayoyi da Amsoshi akan zaman juyayin Abu Abdullahi a.s”