August 7, 2021

Tallafin N1.5bn Daga Bankin Duniya Don Magance Ambaliyar Ruwa A Nasarawa

Daga Idriss Abdullahi 

Mr. Kwa’Kaha Jonathan jami’in gudanarwa na hukumar “NEWMAP” a Jihar Nasarawa yace  Hukumar magance zaizayar-kasa a Najeriya (NEWMAP) zata gina manyan hanyoyin ruwa na kimanin Naira biliyan daya da rabi a kananan hukumomi biyar a jihar Nasarawa don dakile ambaliyar ruwa a jihar.

An kaddamar da aikinn a garin Lafia ranar Juma’a inda Jonathan ya bayyana cewa Bankin Duniya ta tallafawa hukumar NEWMAP domin aiwatar da aikin a jihar Nasarawa domin shawo kan zaizayar kasa da sauran matsalolin muhalli da ake fama da shi a jihar.

Ya ambaci kananan hukumomin da zasu amfana da tallafin wadanda suka hada da Lafia, Keffi, Doma. Nasarawa da kuma Toto, ya kuma bayyana cewa aikin zai kamala cikin watanni hudu.

Gwamnan Jihar, Abdullahi Sule ya kirayi mutanen yankin da za’a aiwatar da wannan aiyuwa da su bada hadin kai ga ma’aikata da ‘yan kwangilar domin kamala aikin ba tare da tsaiko ba. Lamarin matsalolin muhallin dai an dade ana fama da shi sakamakon abubuwan da ke gudana a yankin kamar su Hako, Bola da sauransu.

Kwamishinan muhalli na jihar Musa Ibrahim ya tabbatar da goyon baya da kuma taimakawa da duk abubuwan da suka dace ga hukumar NEWMAP har zuwa karshen wannan aiki.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Tallafin N1.5bn Daga Bankin Duniya Don Magance Ambaliyar Ruwa A Nasarawa”