August 29, 2023

Takun saka tsakanin Nijar da faransa na kara kamari,

Takun saka tsakanin Nijar da faransa na kara kamari, a yayin da wa’adin da sabbin mahukuntan kasar suka baiwa jakadan na faransa a kasar da ya tattara nasa-ye-nasa ya san inda dare ya yi masa cikin sa’o’I 48, ya kawo karshe.

A jiya Litinin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya gabatar da wani jawabi, wanda a cikin sa ya ce duk da matsin lambar sojojin juyin mulki a janhuriyar Nijar, na bukatar jakadan Faransa dake kasar da ya fice ba tare da bata lokaci ba, shugaba Macron, ya umarci jakadan kasarsa Sylvain Itte, da ya ci gaba da kasancewa a Nijar, tare da gudanar da ayyukan sa yadda ya kamata.

Tun a ranar Juma’ar makon jiya ne dai ma’aikatar harkokin waje da hadin gwiwa ta janhuriyar Nijar, karkashin sabbin mahukuntan kasar, ta fitar da wata sanarwa, wadda cikin ta aka umarci jakadan Faransa dake kasar Sylvain Itte, da ya fice daga kasar cikin sa’o’i 48.

Jawabin na Macron, na jiya Litini, ya ci karo da kakkausan martani daga al’ummar aksar ta Nijar, wandanda ke danganta kallaman nasa da girman kai da nuna isa, wanda ba za’a lamunta da shi ba.

A cewar Macron, matsalar ‘yan Nijar a yau ita ce ta sojoji masu juyin mulki, wadanda ke tsaka kasar cikin hadari, saboda sun yi watsai da hanayr dake kan dora kasar bisa ci gaba na tattalin arziki

 

©voh.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Takun saka tsakanin Nijar da faransa na kara kamari,”