TAKAITACCEN TARIHIN IMAM MUHAMMAD AL-JAWAD AT-TAQI(AS):

Imam Muhammad Al-Jawad(as), d’an Imam Ali Ar-Rida(as), d’an Imam Musa Al-Kazim(as), d’an Imam Ja’afar As-Sadiq(as), d’an Imam Muhammad Al-bakir(as), d’an Ali Zainul-Abidin(as), d’an Imam Husain Sayyidus-Shuhada(as); kanin Imam Hasan Al-Mujtaba(as), ‘ya’ya Ali bin Abi Talib(as) da Fatimah Az-Zahra(as); ‘yar Annabi Muhammad(saw).
Al-kunyayarsa: Abu Jaffer al-Thani…
Lakabinsa: At-Taqi, Al-Jawad…
Mahaifiyarsa: Hazrat Bibi Sabika Khatoon, (Khaizuran).
Ranar da aka haifeshi: 10 ga watan Rajab, 195 Hijiriyya. April 12, 811 CE, (809 AD)
Gurin haihuwarsa: Madina.
Farkon imamancinsa: 29 Safar 203/ 9 September 818. (819 – 835 CE).
Wanda ya gajeshi: Ali b. Muhammad al-Hadi(as).
Wanda ya gada: Ali al-Ridha(as).
Tsawon shekarun imamancinsa: 17 years.
Shekarunsa: 25.
Matansa: Samana, Umm al-Fadl.
Yayansa: Ali, Musa, Fatima, Amama.
Lokacin Shahadarsa: 29 ga watan Zul-Qaad 220 H. 29 November 835 CE.
A wata ruwaya; 6 ga watan Dhu al-Hijjah, 220 H.
Gurin da yayi Shahada: Kazmain.
Dalilin Shahadarsa: Gubar da Khalifan Abbasiyawa Mu’atasim yasa aka saka masa.
Gurin da kabarinsa yake: Kazmain, kusa da Baghdad (IRAQ).
Imam Muhammad Jawad(as) shine Jagoran shiriya na 9 cikin jerin jagororin 12 da Annabi Muhammad(saw) ya yi bushara da samuwansu a bayansa, kuma ya bayyana kasantuwarsu da daukakan addinin musulunci, sannan ya rubanya su da Al-kur’ani mai tsarki saboda tsarkakansu, kuma ya yi wasici da yin riko da su gaba daya, kuma ya siffantasu da jirgin tsira; wanda ya hau ya tsira wanda kuma ya saba ya halaka, kofar tuba wanda ya shiga an gafarta masa, hujjojin Allah a bayan kasa, magada ilimin Annabawa da Manzonni, mabubbugar hikima….
An haifi Imam Muhammad Jawad(as) ne a daren jumma’a 10 ga watan Rajab, shekara 195 bayan hijira, a birnin Madinah.
Mahaifiyarsa ita ce Subaikatu wadda ta hada zuriya da Mariyatul-Kibdiyya matar Manzon Allah(saw), wadda ita ce mahaifiyar dansa Ibrahim, kuma ana kiranta da Raihanatu ko Durratu, wanda mijinta Imam Ali Arridha(as) ya ke kiranta da Khaizaran.
Har ila yau: Imam Hasan Al-Askari(as) yana bayyana Subaikatu da cewa an halicceta tsarkakekkiya wadda aka tsarkake. Ana kinawa wa Subaikatu da Ummul-Jawad ko Ummul-Hasan wadda ta kasance mafi daukakan matan zamaninta.
Farin ciki da murna sun lullube Imam Ali Ar-ridha(as) sakamakon haifa masa da mai albarka da Subaikatu ta yi, wanda yake cewa hakika an haifa mini da da ke kama da Musa dan Imrana da ya raba teku gida biyu, kuma mai kama da Isa dan Maryam, Uwar da ta haifeshi ta tsarkaka.
Kyawawan Dabi’un Jagoran Shiriya na 9; Imam Muhammad Jawad(as):
Kasancewar babu makawa mutumin da shi ne jagoran shiriya da Allah Madaukakin Sarki ya daurawa alhaki shiryar da al’ummah zuwa ga hanya madaidaiciya, tare da bambance tsakanin gaskiya da bata, ya zame shi ne mafi sanin mutane a zamaninsa kuma wanda yafi kowa fahimtar al’amuran shari’a da hukunce hukuncen addini, tare da sanin harkokin siyasa da gudanar da al’amuran mutane kuma mafi daukakan mutane a fagen kyawawan dabi’u da cikan kamala. Hakika Imam Muhammad Jawad(as) duk da kasancewarsa mai karancin shekaru a duniya lokacin da ya karbi ragamar jagorancin al’ummah a bayan mahaifinsa, amma ya zame tauraro a fagen ilimi, cikan hankali da kaifin basira wanda ya kera duk wani mai matsayi ko daukaki a zamaninsa.
Malaman fiqihu da masana a fagen fannonin ilimi daban daban da suka jarabashi ta hanyar gudanar da mahawarori da gabatar da tambayoyi masu tsauri gare shi sun samu gamsassun amsoshi da suke yaye shamaki da kawar da duk wani kokwanto da rudu a cikin zukata. Sakamakon haka masana da manazarta suka mika kai ga tabbas da hakika, suka rungume shi a matsayin jagoran shiriya wanda haka ya sanya tafarkin Iyalan gidan manzon Allah(saw) ya kara habaka da watsuwa a tsakanin mutane.
A fagen kyawawan dabi’u kuwa, Imam Muhammad Jawad(as) ya ci gaba da wanzar da dabi’un magabatansa ne da dukkanin rayuwarsu ta zame darasi ga al’ummah, domin sune wadanda suka gaji kyawawan dabi’un kakansu da Allah Madaukakin Sarki ya bayyana shi da cewa:
“Kuma hakika kana kan kyawawan dabi’u masu girma”.
Hakika Imam Muhammad Jawad(as) ya kasance wanda yafi al’umman zamaninsa yawan bautan Allah da biyayya gare shi, matsayinsa a fagen kyawawan dabi’u daidai yake da magabatansa shugabannin shiriya na Iyalan gidan manzon Allah(saw) wadanda suka sadaukar da dukkanin rayuwarsu wajen aikata dukkanin abin da zai kusantar da su ga Allah madaukaki.
Malaman tarihi da mutanen da suka rayu tare da Imam Muhammad Jawad(as) sun bayyana shi da cewa mai yawan salloli ne da tsawaita munajati da mahaliccinsa.
Yazo cikin littafin Mustadrak Awa’limul-Ulum cewa; Imam Muhammad Jawad(as) ya kasance idan sabon wata ya kama ya kan yi sallah ta nafila raka’a biyu, a raka’ar farko yana karanta fatiha da suratul-Ikhlas sau talatin daidai da ranakun wata, sannan a raka’a ta biyu ya karanta fatihah da suratul-Qadir sau talatin, bayan nan ya yi sadaka da abin da ya sauwaka gare shi domin neman amincin watan a wajen Allah madaukakin sarki, kuma kasance yana raya dare da salloli da karatun Al-kur’ani gami da karanta addu’o’i, don haka mutanen da suke tare da shi suka ruwaito tarin addu’o’i da munajatin da yake karantawa.
Haka nan Imam Muhammad Jawad(as) ya kasance mai yawan gudanar da aiki hajji a lokacin rayuwarsa. Imam Muhammad Jawad(as) ya kasance mai yawan kyauta da taimakon mutane wanda saboda tsananin kyautansa da karamcinsa ne mutane suke masa lakabi da Jawad wato mai yawan kyauta da karamci.
Maganganun Yabo Da Aka Yi Kan Imam Muhammad Jawad(as):
Hakika girman matsayi da daukakan da Allah ya huwace wa Imam Muhammad Jawad(saw) sun shige tunanin mutanen da suka yi zamani da shi, saboda haka suka tasirantu da shi zukatansu suka kaunace shi, kuma babu wani da zai zauna ko ya tattauna da shi har sai ya rusuna masa tare da yin furuci da daukakan matsayinsa da shaida kan cancantarsa ga matsayin jagorancin al’ummah zuwa ga hanya madaidaiciya, sakamakon zurfin iliminsa, kaifin basira da zurfin tunaninsa, cikan hankalinsa da kyawawan dabi’unsa.
@Jaridar ahlulbaiti.