April 13, 2023

Ta yaya za a dakile da kandagarkin ciwon zazzabin sauro?

Ranar 25 ga watan Afrilu na ko wace shekara, rana ce ta dakilewa da kandagarkin ciwon zazzabin cizon sauro ta duniya, wadda aka ware a babban taron kiwon lafiya na kasa da kasa karo na 60 a shekarar 2007, da zummar kara azama kan dakilewa da kandagarkin ciwon a duk fadin duniya. Tabbatar da kamuwa da ciwon zazzabin sauro tun da wurwuri da kuma ba da magani kan lokaci, suna iya dakile yaduwar ciwon tsakanin al’umma da kuma hana mutuwar mutane. Hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta yi karin bayani da cewa, yanzu hanya mafi dacewa da ake bi wajen jinyar masu kamuwa da ciwon ita ce, ba da jinya bisa tushen maganin artemisinin. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da hukumar WHO ta yi, an ce, maganin artemisinin ya riga ya kubatar da miliyoyin mutane a duk fadin duniya, tare da jinyar darurruwan miliyoyin mutane a kowace shekara.

A cikin dogon lokaci da kasar Sin ta yi yaki da ciwon zazzabin sauro, ta gano da kuma tace maganin artemisinin daga magungunan gargajiyar kasar Sin, ta kuma tattara da takaita kyawawan fasahohin yaki da ciwon masu dimbin yawa. A ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2021, hukumar WHO ta bai wa kasar Sin takardar shaidar kasa wadda ta kawar da ciwon na zazzabin cizon sauro baki daya. Hukumar ta kuma yaba wa yadda kasar Sin ta kawar da ciwon a baki dayan kasar, bayan da ta dauki shekaru 70 tana kokarin yaki da ciwon ba tare da kasala ba. A shekarun 1940, kasar Sin ta mika rahotannin mutane miliyan 30 masu kamuwa da ciwon a ko wace shekara. A cewar WHO, kasar Sin ta cimma nasara.

Ko da yake ‘yan Adam na yaki da ciwon zazzabin sauro ta mabambantan hanyoyi, amma yadda kwarin plasmodium suke kin jin magani, yana illata kokarin da ake yi.

Hukumar WHO ta nuna cewa, a shekarun baya, an rage sauri ko kuma dakatar da aikin rage kudin da ake kashewa kan shawo kan ciwon zazzabin sauro a duniya, musamman ma a yankin Afirka da kudu da hamadar Sahara. Ana bukatar daukar matakan bai daya cikin gaggawa, a kokarin mayar da duniya kan hanyar cimma manufar WHO ta manyan tsare-tsaren fasaha ta dakilewa da kandagarkin ciwon a shekarar 2030.

Hukumar WHO ta fito da manyan tsare-tsaren fasahar yaki da ciwon zazzabin sauro daga shekarar 2016 zuwa 2030 don tabbatar da kawar da ciwon baki daya a duniya. Bisa tanade-tanaden da ke cikin wannan takardar, an ce, ya zuwa shekarar 2030, kamata ya yi kasashen duniya su rage yawan masu kamuwa da ciwon da kuma yawan mamata sakamakon ciwon har a kalla kashi 90 cikin na shekarar 2015.

Yaya lamarin yake a kasashe masu tasowa kamar kasarmu Nageriya?

 

SHARE:
Kiwon lafiya 0 Replies to “Ta yaya za a dakile da kandagarkin ciwon zazzabin sauro?”