September 2, 2021

Sujjada Akan Turba

Cigaba daga runutun baya…

Wasu kuma sukan ce: Shin qasar Karbala ta fi qasar Makka da ta Madina wadda take dauke da jikin manzon Allah (s.a.w)?

Babu shakka qasar Makka da Madina suna a wani matsayi wanda ya bambanta da na Karbala, wannan kuma ba yana nufin imam Husaini ya fi kakansa manzon Allah ba, domin kuwa girman imam Husaini wani sashe ne daga girman manzon Allah (s.a.w), kuma daukakarsa da matsayinsa a wajen Allah ya faru ne sakamakon kasantuwarsa imami a cikin addinin kakansa (s.a.w), don haka matsayin ba wani abu ba ne daban face wani bangare na manzon Allah (s.a.w), sai dai yanayin da aka kashe imam Husaini (a.s) shi da iyalan gidansa da na ‘yan uwansa da sahabbansa saboda tsayar da addinin Musulunci da tabbatar da asasinsa tare da kare shi daga wasan ma’abota sha’awa da barna sai Allah (T) ya musanya masa wannan shahada tasa da abubuwa guda uku:

1 – Allah yana amsa addu’ar da aka yi a qarqashin qubbarsa (a.s).

2 – Allah ya sanya imamai a zuriyarsa.

3 – Allah ya sanya waraka a cikin turbarsa.

An ruwaito daga Muhammad dan Muslim ya ce: Na ji aba Ja’afar da Ja’afar dan Muhammad (a.s) suna cewa: “Haqiqa Allah (T) ya yi wa imam Husaini (a.s) musaya daga kisansa: Ya sanya imama a zuriyarsa, ya sanya waraka daga turbarsa, (kuma) yana amsa addu’a a wajen kabarinsa . . .

Biharul Anwar na Majlisi

Haqiqa Allah (T) ya girmama imam Husaini (a.s) saboda kisan da aka yi masa mafi munin kisa, wanda banu Umayya suka haxa iyalan annabi Muhammad (s.a.w) rankatakaf suka nemi qarar da su daga ban qasa, kai har jarirai ba su bari ba (sai dai ta Allah ba tasu ba!) Bayan kashe su aka yi sukuwa a kan gawarwakinsu, aka tsintsinke kawunansu, sannan aka kame matansu a matsayin fursunan yaqi da wanin wannan na daga masifu da suka gani saboda tsayar da addini, shin wannan bawa na Allah bai cancanci girmamawa irin wannan ba?

Girmama turbar imam Husaini (a.s) girmama shi ne, kuma girmama shi girmama manzon Allah ne, girmama manzon Allah kuwa girmama Allah (T) ne, Allah (T) yana cewa: (ومن يعظم شعائر الله فإنها من تقوى القلوب)   Girmama alamomin Allah yana daga cikin taqawar zukata

SHARE:
Makala 0 Replies to “Sujjada Akan Turba”