August 22, 2021

SUJJADA A KAN TURBA

Daga Mujtaba Adam

Babu shakka dukkan malaman Musulmi sun hadu a kan ingancin yin sujjada a kan qasa da dangoginta ba tare da togaciya ba, amma abin mamaki sai aka samu wani sashe na Musulmai suke jefa ishkali tare da yin zargi a bisa zato game da yin sujjada a kan turba musamman turba Husainiyya da cewa wani nau’i ne na shirka, wato yin sujjada ga wanin Allah. Wannan ba wani abu ba ne face sharri da qage, domin duk wanda ya dubi sujjada zai ga cewa dayan abu biyu ne:

1 – Yi wa wani abu sujjada.

2  Yin sujjada a kan wani abu.

Bambanci tsakanin wadannan abubuwa biyu shi ne: Yi wa wani sujjada yana daga cikin nauoin shirka matuqar wanda ake wa sujjadar ba Allah ba ne; A lokacin da yin sujjada a kan wani abu ke nufin dora goshi a kan abin domin yi wa wani sujjada. Kuma ya wajaba sujjadar ta kasance ga Allah taala, ba a kan Allah ba, domin yin sujjada a kan Allah kafirci ne tsantsa.

To a lokacin da yan Shia suke dora goshinsu a kan turba a cikin salla ba suna nufin yi wa turbar sujjada ba ne, suna yin sujjadar ne a kanta da nufin yi wa Allah madaukakin sarki sujjada suna masu tsarkake shi. Wanda fatawoyin malamansu cike yake da haramcin yin sujjada ga wanin Allah madaukaki.

Ga kadan daga cikin fatawoyin malaman game da yin sujjada ga wanin Allah taala:

1 – Sayyid Yazdi ya fada a cikin littafinsa Alurwatul wusqa’: Ya haramta a yi sujjada ga wanin Allah, domin sujjada ita ce qarshen qasqantar da kai ga wanda yake mafi girma da daukaka (wato Allah taala).

2 – Sayyid Khui ya fada a cikin littafinsa: Minhaj Assalihin 1: Ya haramta a yi sujjada ga wanin Allah, babu bambanci tsakanin (wannan din) ma’asumi ne ko waninsa.

Shia a sujjadarsu suna misaltuwa da qololuwar bauta da qasqantar da kai ga Allah madaukaki, abin da ke tabbatar da hakan shi ne adduoin da suka samu daga Ahlulbaiti (a.s), kuma suke ta nanata su a sujjadarsu tare da narkewa a cikin lamarin Allah.

Ga kadan daga cikin adduoin:

1 – (سبحان ربي الأعلى وبحمده) Tsarki ya tabbata ga ubangijina madaukaki tare da gode masa.

 

2 –  (لا إله إلا الله حقا حقا، لا إله إلا الله إيمانا وتصديقا، لا إله إلا الله عبودية ورقة، سجدت لك يارب تعبدا ورقة لا مستنكفا ولا مستكبرا، بل أنا عبد ذليل خائف مستجير).

Tabbas babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, tabbas da gaske babu abin bauta da gaskiya sai Allah cikakkiyar bauta da miqa wuya. Na yi maka sujjada ya ubangiji domin bauta maka tare da miqa wuya babu girman kai, sai dai ni qasqantaccen bawa ne wanda yake cike da tsoro da neman mafaka.

3 – (اللهم لك سجدت وجهي وبك آمنت، ولك أسلمت وعليك توكلت، وأنت ربي، سجد وجهي للذي خلقه وشق سمعه وبصره والحمدلله رب العالمين، تبارك الله أحسن الخالقين).

Ya Allah domin kai fuskata ta yi sujjada, na yi imani da kai, gare ka na miqa wuya, kuma da kai na dogara, kai ne ubangijina. Fuskata ta yi sujjada ga wanda ya qaga mata ji da gani, godiya ta tabbata ga ubangijin talikai, madalla da ubangijin da yake kyautata halitta.

Wata qila wani ya ce: To ai yan Shia suna girmama turba Husainiyya, kamar sumbantarta tare da ba ta kulawa, wannan yana jefa shakka da zaton cewa bauta mata suke yi?!

Da farko wannan yanayin da aka fada ai ba abu ne da sharia ta haramta shi ba, idan ba haka ba sai mu ce: Dukkan Musulmai suna girmamawa tare da kulawa da Alqurani ko gafakarsa da Kaaba da Hajarul Aswad kuma suna sumbantarsu, shin su ma bauta musu ake yi?

A lokacin da yan Shia suke sumbantar turba Husainiyya suna misalta so da qauna ne ga jikan manzon Allah (s.a.w) imam Husaini (a.s), kamar yadda tarihi ya tabbatar da cewa annabi (s.a.w) shi ne ya fara sumbantar wannan turba tsarkakakkiya.

1 – Hakim Nisabori ya ruwaito a cikin Mustadraku Assaahihaini1 daga Ummu Salama (r.a) cewa: Manzon Allah (s.a.w) yana kwance sai ya farka a razane, sai ya sake komawa, ya sake farkawa a razane, ya sake komawa sai ya sake farkawa tare da jar qasa a hannunsa yana sumbantarta, sai na ce: Wannan qasar fa ya maaikin Allah?

Ya ce: Jibrilu ya ba ni labarin cewa za a kashe wannan dan a qasar Iraki. Sai na ce da jibrilu ya nuna min qasar da za a kashe shi, wannan ita ce qasar . . .

Sai Hakim ya ce: Wannan hadisin ingantacce ne a bisa sharudan Bukhari da Muslim amma ba su  fitar da shi ba.

2 – Ahmad dan Hambali ya fitar a cikin Musnadinsa j6 / 294, daga Ummu Salama ko Aisha daga manzon Allah (s.a.w) ya ce: Haqiqa malaika ya shigo min ya ce da ni: Lallai wannan dan naka za a kashe shi, idan kana so sai in nuna maka qasar da za a kashe shi a kanta, sai ya fito da wata qasa mai fatsi-fatsi.

3  Hafiz Haisami ya ruwaito a cikin littafin Majmau Azzawaid j 9 / 190, daga (imamu) Ali (a.s) ya ce: Na shiga wajen manzon Allah (s.a.w) wata rana sai na tarar idanuwansa na zubar hawaye, sai na ce: Ya manzon Allah shin wani ya bata maka na ga idaniyarka na zubar hawaye? Sai ya ce: Jibrilu ne ya tashi daga wurina, ya ba ni labarin cewa za a kashe Husaini a filin Furat. Sai ya ce: Shin kana son in nuna maka qasar? Sai na ce: Naam. Sai ya miqa hannunsa ya damqo qasa ya ba ni ita, ban iya mallakar idanuna ba sai da suka zubar da hawaye.

4  Siyudi ya ruwaito a cikin littafin Khasaisul Kubra, a cikin: Babu ikhbarun nabiyi biqatlil Husaini (a.s)’  kimanin hadisai ashirin daga manyan malamai daga amintattun malaman Ahalissunna waljamati. Kamar: Hakim da Baihaqi da Abi Naim da wasunsu, daga Ummu Salama da Ummu Fadl da Aisha da Ibni Abbas da Anas da suke qarfafa labarin turba da malaika Jibriu ya zo wa manzon Allah (s.a.w) da shi.1

 

 

Wasu sukan ce: To me ya sa sai turbar imam Husaini?

A biyo mu don gamsassun hujjoji a rubutu na gaba…

 

 

SHARE:
Makala, Shubuhohi Da Raddodin Su 0 Replies to “SUJJADA A KAN TURBA”