August 1, 2021

SUFETO JANAR NA ‘YAN SANDA YA BUKACI DAKATAR DA ABBA KYARI

Daga Abbas Idriss

A ranar Lahadi, 1 ga watan Augusta ne Babban Sufetan ‘yan Sanda Usman Baba ya bukaci dakatar da Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari bisa zargin da ake yi masa na karbar cin-hanci daga Hushpuppi wanda ake zargi da laifin damfara.

A ‘yan kwanakin da suka gabata shi mataimakin kwamishinan ya kore zargin da ake yi masa na karbar cin-hancin, amma kotu ta bada umarnin bincikarsa ta hanyar hukumar FBI.

A rahoton da ya fita daga shi Babban Sufeton ta hanyar mai Magana da yawun hukumar ‘yan sanda ya bukaci gaggauta dakatar da Mataimakin Kwamishinan ‘yan Sanda Abba Kyari.

A yadda ya bayyana a bayanin sa, dakatar da Jami’in zai bada damar bincike yadda ya dace ba tare da wani tsaiko ba , sannan kuma ya bayyana bincken zai gudana ta hanyar da ya dace ba tare da tauye hakkin shi jami’in ba a tsahon lokacin da za’a dauka a binciken.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “SUFETO JANAR NA ‘YAN SANDA YA BUKACI DAKATAR DA ABBA KYARI”