August 26, 2023

​Sudan: Sojojin Sudan Sun Kai Hari Kan Mayakan RSF A Tsakiyar Birnin Khartum Babban Birnin Kasar

Labaran da suke fitowa daga kasar Sudan sun bayyana cewa a yau Asabar an ji karar fashewa bai karfi a tsakiyar birnin Khartum babban birnin kasar, kuma an ga harshen wuta ya tashi sama sosai a tsakiyar birnin.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta kasar Qatar ta bayyana cewa sojojin kasar ne suka kai hari kan dakarun ‘Rapid Support Forces (RSF)’.

Labarin ya kara da cewa harin ya fada kan runbun ajiyar makamai ne da ke unguwar da damakrun RSF suke iko da shi a cikin birnin. Wata majiyar kuma ta bayyana cewa mai yuwa hare-haren sojojin ya fara kan makamashin jiragen sama da suke kusa da tashar jiragen sama na birnin ne.

Wasu sanana harkokin tsaro sun bayyana cewa mai yuwa hukumar leken asiri ta M16 na gwamnatin kasar Burtaniya tana tallafawa wani bangare a cikin yakin da ke faruwa a kasar Sudan.

 

©voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Sudan: Sojojin Sudan Sun Kai Hari Kan Mayakan RSF A Tsakiyar Birnin Khartum Babban Birnin Kasar”