April 19, 2023

​Sudan: RSF Ta Sanar Da Amincewa Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Na Sa’o’i 24

 

Dakarun RSF na Sudan sun sanar a yau Laraba cewa an amince da tsagaita bude wuta na sa’o’i 24.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta shafin Twitter ta ce: “An amince da tsagaita bude wuta na sa’o’i 24, daga karfe shida na yammacin yau Laraba, 19-4-2023, har zuwa karfe shida na yamma gobe Alhamis, 20-4-2023.”

Sanarwar ta tabbatar da cewa dukkanin bangarori sun amincewa da yarejejniyar ta tsagaita bude wuta, tare da yin fatan cewa daya bangaren zai mutunta ta a daidai lokacin da aka sanar.

Tun da farko dai, rundunar sojin Sudan ta ce dakarunta na ci gaba da kai farmaki a rana ta biyar a jere, domin tunkarar wani sabon hari a kusa da ofishin babban hafsan hafsoshin sojin kasar, wanda ya jawo asarar mai yawa ga daya bangaren, tare da lalata wasu motocin yaki da dama.

An shafe makonni ana takun saka tsakanin Muhammad Hamdan Dagalo, wanda ke jagorantar dakarun Rapid Support Forces, da Abdel Fattah al-Burhan, babban kwamandan sojojin Sudan, wadanda tare suka kawar da farar hula daga mulki a wani juyin mulki a watan Oktoban 2021, kafin rikicin siyasa da neman iko a tsakaninsu ya rikide zuwa fada a ranar Asabar da ta gabata.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Sudan: RSF Ta Sanar Da Amincewa Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Na Sa’o’i 24”