Sudan : Rikici Ya Sanya Mutane 700,000 Barin Muhalensu A Cikin Gida

Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa sama da ‘yan Sudan 700,000 ne rikicin kasar ya tilastawa tsarewa daga gidajensu, baya ga wasu 150,000 da tunu suka yi hijira zuwa kasashe makobta.
Hakan ya linka wadannan alkalumman idan aka kwatanta da ranar Talata data gabata, a daidai lokacin da aka kai ga rasa mafita game da rikicin kasar inji MDD.
Rikicin na Sudan da ya shiga kwana na 25, na faruwa ne tsakanin janar janar masu fada a ji a kasar ta Sudan da suka hada da babban hafsan sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhane, da kuma Janar Mohamed Hamdane Daglo, na rundinar kai daukin gaggawa ta RSF.
Masana na ganin akwai yiyuwar fararen hula su dauki makamai a rikicin dake faruwa a kasar wanda kuma babban barazana ne ga kasra dama yankin.
A halin da ake ciki dai jami’in MDD, mai lura da harkokin jin kai Martin Griffiths, ya bukci bangarorin dake rikici a kasar dasu samar da hanyoyin shigar da kayan agaji kamar yadda kakakinsa Farhan Haq ya sanar.
Kawo yanzu mutane sama da 750 ne aka rawaito sun rasa rayukansu tun barkewar rikicin kasar a ranar 15 ga watan da ya gabata, kana wasu 5,000 suka jikkata.