April 30, 2023

​Sudan: Mayakan “Daukin Gaggawa” Na Kasar Sudan Sun Bada Sanarwan Kakkabo Jirgin Saman Yakin Sojojin Kasar

 

A dai dai lokacinda sojojin ‘daukin gaggawa’ na kasar Sudan suke bada sanarwan kakkabo jirgin saman yakin sojojin kasar a shugaban gwamnatin sojojin kasar Sudan Abdul Fattah Al-burhan ya bada sanarwan cewa gwamnatinsa tana kan bakanta na mika mulki ga fararen hula kuma bayan goyon bayan wata kungiyar siyasa ko wata kungiya a kasar a shirin mikawa fararen hula shugabancin kasar.

Amma shugaban dakarun ‘daukin gaggawa’ Muhammad Hamdan Doqlo ya zargi shugaban Burhan da kokarin hana mika mulki ga fararen hula da kuma labarin cewa duk abinda yake fada dangane da wannan shirin ba gaskiya ne ba.

A wani bangaren kuma bangarorin biyu masu fafatawa da juna a kasar ta Sudan sun zabi wakilansu don neman hanyoyin warware rikicin kasar wacce a halin yanzu ya kai kimani makonni biyu kenan . Sun kuma bukaci halattar gwamnatin Sudan ta Kudu a duk wata tattaunawa don fita daga matsalolin da kasar take fama da su.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Sudan: Mayakan “Daukin Gaggawa” Na Kasar Sudan Sun Bada Sanarwan Kakkabo Jirgin Saman Yakin Sojojin Kasar”