August 29, 2023

Sudan : Janar Al-Burhan, Ya Yi Watsi Da Duk Wata Tattaunawa Da Dakarun RSF

Babban hafsan sojin Sudan ya yi watsi da duk wata tattaunawa da rundinar dakarun kai daukin gaggawa ta RSF a kasar, tare da shan alwashin samun nasara kan dakarun.

Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda kuma shi ne shugaban kasar, ya ce “ba mu, ba yarjejeniya da ‘yan cin amanar kasa”.

Kalamman nasa dai na matsayin maida martani ne ga rundunar ta RSF wacce ta ce a shirye take domin gudanar da tattaunawar da za ta haifar da cikakken sulhu.

Shugaban dakarun na RSF, Laftanar Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti ne ya fitar da wani dogon bayani a ranar 27 ga watan Agustan nan a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter, yana mai cewa “shirye suke domin kawo karshen tashin hankali da kuma sake gina wata sabuwar kasar Sudan”.

Hemedti, ya ce kawo karshen yakin “zai dora kasar a kan turbar zama kasa mai bin tsarin dimukuradiyya.

Wannan na zuwa ne rana daya da shugaban sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya isa wani birnin gabashin kasar a karon farko, tun bayan barkewar rikicin a watan Afrilun da ya gabata.

 

©voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sudan : Janar Al-Burhan, Ya Yi Watsi Da Duk Wata Tattaunawa Da Dakarun RSF”