September 18, 2021

SOKOTO: Yan Bindiga Sun Kai Hari Tangaza, Sun Kashe Mutum 1 Tare Da Garkuwa Da Mutane Da Dama

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Hukumar yan sandan jahar Sokoto a yau ta tabbatar da kai harin yan bindiga a karamar hukumar Tangaza na jahar Sokoto inda suka hallaka mutum guda har lahira kana kuma suka yi awun gaba da wasu mutane da dama zuwa sansanin su.

Mai magana da yawun hukumar yan sanda ASP Sunusi Abubakar ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a jahar Sokoto, ya kuma bayyana cewa harin ya faru ne da yammacin jiya Juma’a.

Yayi karin bayani cewa sun kashe wani dan kasuwa guda kana kuma suka yi garkuwa da mutanen da har yanzu ba’a gama tabbatar da adadin su ba, kana a kokarin su na aiwatar da hakan sun yi awun gaba da kayayyakin masarufi na daga abinci da kuma lemon roba.

Ya kuma kara da cewa har zuwa yanzu, hukumar su tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro suna kan binciken lamarin.

Sai dai kuma wata majiya daga cikin garin na Tangaza ya bayyana cewa bayan kashe dan kasuwan akwai kuma karin wata yarinya wacce ta rasu a yayin da ake kokarin yi mata magani a asibiti.

Jami’in ya kara da cewa akwai wasu karin mutane uku da suka samu raunuka kuma yanzu haka suna asibiti don magani

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “SOKOTO: Yan Bindiga Sun Kai Hari Tangaza, Sun Kashe Mutum 1 Tare Da Garkuwa Da Mutane Da Dama”