December 8, 2021

Sokoto: Yadda ‘yan bindiga suka ‘kone fasingogin wata mota har lahira

Daga Muhammad Bakir Muhammad


 

Rahotanni daga jihar Sokoto na nuna cewa yan bindiga sun kone wasu matafiya har lahira a kauyen Gidan Bawa dake karamar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto.

Rahotonnin sun bayyana cewa matafiyan na kan hanyar su ne zuwa Gadan Gayan dake jihar Kaduna don ketarawa zuwa kudancin kasar Nijeriya saboda neman halaliyar su.

Rahoton ya nuna cewa yan bindigan sun tare motar ne a yayin da take tsaka da tafiya, kana kuma suka bude mata wuta.
Lamarin dai ya faru ne a kauyen Keke dake yankin Gidan Bawa da misalin karfe 10 na safiyar Litinin.

Wasu daga shaidu sun ce, yan bindigan sun fara ne da harbin tayar motar, inda daga nan motar ta fara ci da wuta.

Daga wannan matakin ne ‘yan bindigan suka kewaye motar don su tabbatar da babu wani fasinja da ya fita daga motar, alhali motar na tsaka da cin wuta.

Wani rahoton ya bayyana cewa fasinjoji 10 ne ke cikin motar, amma babu mutum ko guda da ya tsira da rayuwarsa.

Dan majalisar jiha mai waliktan Sabon Birni a jihar Sokoto, Ibrahim Sa’idu a yayin tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa ‘yan bindigan na kwacen wayoyi, ababen hawa da kuma sauran abubuwa masu daraja yanzu.

Ya kuma Kara da cewa, ba da jimawa ba sun saci mutane 9 a kauyen Masawa.

Wani daga mazauna yankin ya bayyana cewa a yanzu haka an zuba jami’an tsaro a yankin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Sokoto: Yadda ‘yan bindiga suka ‘kone fasingogin wata mota har lahira”