September 19, 2021

Sokoto: Yadda Matasa Suka Kona Yan Bindiga A Garin Tangaza

Daga Muhammad Bakir Muhammad


A jiya Asabat ne wasu fusatattun matasa suka kutsa cikin helkwatan yan Sanda a karamar hukumar Tangaza dake jahar Sokoto inda suka kashe wasu mutane 13 da ake zargin yan bindiga ne da ke kulle cikin chaji ofis din yan sandan kana kuma suka kona gawarwakin su zuwa toka.

Wata majiya ta bayyana cewa yan bindigan da aka kona din na daga cikin wadanda suka shiga garin suka yi aiwatar da kisa a ranar juma’a da misalin karfe 8 na dare.

Kamar dai yadda muka wallafa a jaridar mu ta AHLULBAITI a rahotannin ranar Asabat, bayanai sun tabbatar da cewa bayan kisan mutane biyu yan bindigan sun yi awun gaba da wasu mutanen kana kuma a tare da su sun tafi da kayayyakin masarufi da suka hada da abinci da abubuwan sha. Inda daga baya jami’an tsaro suka samu rahoto kana suka bi diddigin su.

A samamen da jami’an tsaron suka kai a washe garin aukuwar lamarin, sun sami nasarar cafke wasu daga cikin yan bindigan a dajin Tangaza inda suka turo keyar su zuwa helkwatan yan sanda na garin, ba a iya nan kadai ba, an yi nasarar dawo da abubuwan da suka sata na daga kayayyakin masarufi.

Mazauna garin sun bayyana cewa bayan kawo yan bindigan zuwa helkwatan na yan sanda ba tare da wani bata lokaci ba dandazon matasa suka afka helkwatan inda suka ci karfin yan sandan sannan suka kashe dukkanin yan bindigan guda 13 kana kuma suka cinna wuta kan gawarwakin su.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa ganin yanayin da mutanen yankin suke na nuna alamar a shirye suke da kare kansu da dukkan karfin su daga yanzu, ya kuma ce bayan faruwan lamarin an jibge jami’an yan sanda da dama a garin.

A bayanin da aka samu daga mai magana da yawun hukumar yan sandan jahar Sokoto ya tabbatar da faruwar lamarin duk da cewa bai zurfafa bayani kan yadda lamarin ya faru ba.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Sokoto: Yadda Matasa Suka Kona Yan Bindiga A Garin Tangaza”