May 29, 2023

Sojojin Syria Sun Kakkabo Makamai Masu Linzami Da HKI Ta Harba A Kusa Da Birnin Damascuss

 

Majiyar sojojin Syria sun sanar da cewa da misalin karfe 11: 45 na daren jiya ne jiragen yakin HKI su ka harba makamai masu linzami daga yankin tuddan Gulan zuwa kan kusa da birnin Damascuss, sai dai makaman kasar Syria sun yi nasarar kakkabo da dama daga cikinsu.

Majiyar ta kara da cewa harin na ‘yan sahayoniya ya haddasa asarar dukiya,amma babu ta rayuka.

Jiragen yakin HKI sun saba kai hare-hare a kan garuruwa da cibiyoyi daban-daban na kasar Syria da a wasu lokutan suke haddasa asara ta rayuka da dukiya.

A farkon wannan watan na Mayu ma dai jiragen yakin HKI sun kai kwatankwacin wannan harin a kan garin Halab da lallata filin saukar jiragen sama na kasa da kasa dake birnin.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sojojin Syria Sun Kakkabo Makamai Masu Linzami Da HKI Ta Harba A Kusa Da Birnin Damascuss”