January 17, 2023

Sojojin Somaliya Sun Kwace Iko Da Birnin Haradhere Daga Hannun Al-Shabab

Firaministan kasar Hamza Abdi Barre ya bayyana kwace garin na Haradhere da ke tsakiyar jihar Galmudug a matsayin nasara mai cike da tarihi. Ya ce an murkushe makiyan kasar.

Kwacewar tashar ruwan da hanyoyin shigar da kayayyaki, babbar hasara ce ga kungiyar Al Shabaab.

A watannin baya-bayan nan, kungiyar ta rasa wasu muhimman yankuna a fafatawa da dakarun gwamnati.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Sojojin Somaliya Sun Kwace Iko Da Birnin Haradhere Daga Hannun Al-Shabab”