December 4, 2023

Sojojin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabab 60 a yankin tsakiyar kasar

A safiyar jiya Lahadi ne sojojin kasar Somaliya (SNA) suka kashe mayakan al-Shabab 60 tare da raunata wasu da dama a wani farmakin hadin gwiwa da suka kai kusa da garin Halgan da ke tsakiyar kasar Somaliya, a cewar gwamnatin kasar.

Sanarwar da ma’aikatar yada labarai, al’adu da yawon bude ido ta kasar ta fitar a Mogadishu, babban birnin kasar ta bayyana cewa, an kai harin ne kan ‘yan ta’addan al-Shabab da kwamandojinsu da ke hada gangami domin kai hari a yankunan tsakiyar kasar Somaliya.

SNA da abokan hadin gwiwa na kasashen duniya sun kuma lalata sansanonin ‘yan ta’adda da makamai da dama a yankunan. Sojojin na ci gaba da bin sawun ‘yan ta’addan da suka tsere daga wurin, a cewar ma’aikatar.

Kungiyar ta al-Shabab dai ba ta ce komai ba game da sabon harin da sojojin suka kai.

 

© Cri Hausa

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sojojin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabab 60 a yankin tsakiyar kasar”