April 27, 2023

Sojojin Nigeria 5 Sun Mutu A Sanadiyyar Tashin Wata Nakiya A Jihar Borno

 

Sojojin dai suna yin ran-gadi ne a kauyen Laayi dake kusa da garin Damasak-dake kan iyaka da jamhuriyar Nijar- a yayin da wata nakiya da aka ajiye a gefen hanya ta tarwatse.

Wani farar hula mai aiki da jami’an tsaron kasar a fada da ‘yan ta’adda mai suna Babakura Kolo ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa; Kungiyar nan ta ISwap ce ta kai harin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5.

A gefe daya, wata majiyar ta bayyana cewa, masu ikirarin jihadin sun kai hari a garin na Laayi, inda su ka sace mutane hudu da su ka hada da dagacin garin.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani da ya fito daga sojoji dake yankin.

Yankin Arewa maso gabashin kasar ta Nigeria dai ya dauki shekaru 14 yana fuskantar hare-hare daga kungiyoyi masu dauke da makamai da su ka hada Boko Haram, da kuma Iswap daga baya.

Daga barkewar rikicin a 2009 zuwa yanzu an kashe fiye da mutane 40,000, yayin da wasu miliyoyi su ka zama ‘yan gudun hijira.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sojojin Nigeria 5 Sun Mutu A Sanadiyyar Tashin Wata Nakiya A Jihar Borno”