November 18, 2022

Sojojin Najeriya sun hallaka ’yan ta’adda 50 a arewacin kasar

Rundunar sojojin Najeriya ta ce cikin makwanni 2 da suka gaba, dakaruta sun hallaka a kalla ’yan ta’adda 50, yayin wasu hare-hare da suka kaddamar a yankin arewacin kasar.
Mai magana da yawun rundunar Musa Danmadami, ya shaidawa manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar cewa, yayin samamen da sojojin suka gudanar, sun kubutar da sama da mutane 50, da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su a sassan arewa maso yamma, da arewa maso gabashin kasar.
Danmadami ya kara da cewa, sojoji na kara fatattakar ’yan ta’adda ta sama da kasa, domin kakkabe gyauronsu, ciki har da mayakan Boko Haram da na ISWAP, dake da sansanoni a yankin jihar Borno ta arewa maso gabashin kasar.
Kaza lika jami’in ya ce tsakanin ranakun 4 zuwa 5 ga watan Nuwamban nan, sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka wasu fitattun kwamandojin kungiyar ISWAP, yayin wani hari ta sama, a yankin karamar hukumar Bama ta jihar Borno, ciki har da Ali Kwaya, da MallamBukar Mainoka.

©cri(Saminu Alhassan)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sojojin Najeriya sun hallaka ’yan ta’adda 50 a arewacin kasar”