May 27, 2024

sojojin Masar sun yi luguden wuta kan sojojin Isra’ila a mashigar Rafah,

Tashar talabijin ta ta Isra’ila ta bayar da rahoton wani lamari da ba a saba gani ba tsakanin sojojin mamaya na Isra’ila da sojojin Masar a mashigar kan iyakar Rafah, lamarin da ke nuni da irin tasirin da siyasa ke da shi a cikin tashin hankali.

Tashar talabijin ta Isra’ila ta bayyana cewa, sojojin Masar sun yi luguden wuta kan sojojin Isra’ila a mashigar Rafah, ba tare da samun wani rauni ba. Kazalika, kafofin yada labaran Isra’ila sun ruwaito cewa IOF ya mayar da martani da harbin gargadi. An kuma tabbatar da cewa binciken da sojoji ke yi na IOF ya janye duk wani labari game da lamarin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na KodKod na Isra’ila ya bayar da rahoton cewa, ba a samu asarar rai ba a tsakanin sojojin na Isra’ila amma ya bayyana cewa an kashe sojojin Masar biyu. Sai dai jaridar Ynet ta Isra’ila ta yi ikirarin cewa sojan Masar daya ya rasa ransa yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon arangamar.

Bayan haka, wakilin Al Mayadeen ya ruwaito yarjejeniyar kafa kwamitin da zai binciki lamarin. A halin da ake ciki kuma, kakakin sojojin mamaya na Isra’ila ya tabbatar da ci gaba da gudanar da bincike tare da tuntubar bangaren Masar.

 

AL-MAYADEEN

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “sojojin Masar sun yi luguden wuta kan sojojin Isra’ila a mashigar Rafah,”