January 21, 2023

Sojojin Isra’ila Sun Bindige Wasu Falasdinawa 2 Har Lahira.

Kafofin yada labaran Falasdinu sun rawaito cewa dakarun sojin Isra’ila sun kutsa kai cikin sansanin a safiyar wannan Alhamis, lamarin da ya haifar da kazamin fada da mazauna yankin.

An bayyana mutanen biyu da aka kashe da Jawad Bawatqa mai shekaru 58 da kuma Adham Jabarin mai shekaru 26.

kisan na baya-bayan nan ya sanya adadin Falasdinawa da sojojin Isra’ila suka kashe daga farkon shekarar nan ta 2023 zuwa 17, ciki har da yara hudu.

Sojojin na Isra’ila dai sun kaddamar da hare-hare a garuruwa daban-daban na yankin yammacin kogin Jordan da suka mamaye kusan kowace rana bisa abinda suka kira “farautar Falasdinawan da ake nema’’, almarin dake haifar da mumunar arangama da mazauna yankunan.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Sojojin Isra’ila Sun Bindige Wasu Falasdinawa 2 Har Lahira.”