May 10, 2023

​Sojojin HKI Sun Rusa Makarantar Firai Mari A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

 

Sojojin HKI sun rusa wata makarantar firaimari ta falasdinawa a safiyar yau Lahadi a kusa da garin Bethlahm na yankin yamma da kogin Jordan.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto majiyar gwamnatin falasdinawa na cewa wannan bas hi ne karon farko wanda yahudawan suke take hakkin ilmantarwa na yara falasdinawa ba.

Majiyar ta kara da cewa da farko sojojin yahudawan sun yiwa makarantar kawanya sannan a gaban idonsu sai da suka tabbatar da cewa motar buldoser ta rusa gineginen makarantar gaba daya.

Majiyar ta kara da cewa kafin haka sojojin yahudawan sun rusa makarantar a shekara ta 2017 amma aka sake gina shi a wanacan shekarar.

Gwamnatin HKI dai ta tana ci gaba da rusa gine-gine Falasdinawa kama daga gidaje kwana, makarantu da kasuwanni da sunan an ginasu ba bisa ka;id aba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Sojojin HKI Sun Rusa Makarantar Firai Mari A Yankin Yamma Da Kogin Jordan”