March 31, 2024

Sojojin HKI Sun Jikkata Masu Sa Ido Na MDD Akan Iyaka Da Lebanon

A wani hari da sojojin HKI su ka kai akan wata mota dake tafiya a kudancin Lebanon mai dauke da jami’an sa ido na MDD

A wani hari da sojojin HKI su ka kai akan wata mota dake tafiya a kudancin Lebanon mai dauke da jami’an sa ido na MDD  a kusa da Rmeish sun jikkata ma’aikatan biyu da kuma wasu jami’an tsaro biyu.

Kamfanin dillancin labarun Reuters ta ambato wani daga cikin jami’an tsaron yana cewa; motar tana dauke da injiniyoyi masu sanya idanu da kuma dan kasar Lebanon aya da yake aikin fassara.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da sojojin HKI su ke kai  wa dakarun MDD na zaman lafiya ( UNIFI) hari, inda a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata su ka jikkata masu aikin sintiri.

V.o.h

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Sojojin HKI Sun Jikkata Masu Sa Ido Na MDD Akan Iyaka Da Lebanon”