August 30, 2023

​Sojoji Masu Juyin Mulki A Gabon Suna Tsare Da Dan Tsohun Shugaban Kasar Saboda Cin Amanar Kasa

Sojojin wadanda suka yi juyin mulki a kasar Gabon sun bada sanarwan cewa suna tsare da Ondimba Ali Bongo dan tsohon shugaban kasar wanda suka yiwa juyin mulki a safiyar yau talata, sun kuma bayyana cewa suna tuhumar Ondimba da laifin cin amanar kasa.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar Ali Bongo yana daurin talala a cikin gidansa tare da iyalansa da kuma likitansa tun bayan da suka yi masa juyin mulki.

Sojojin sun bayyana cewa sun bata sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata wanda Ali Bongo ya lashe, sun kuma rufe dukkan kan iyakokin kasar. Banda haka sun bayyana cewa sun dauki wannan matakin ne da izinin rundunar sojojin kasar.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Sojoji Masu Juyin Mulki A Gabon Suna Tsare Da Dan Tsohun Shugaban Kasar Saboda Cin Amanar Kasa”