SIRRINSAMUN NASARA MATAKI NA UKU YIN AIKI DA JAJIRCEWA

SirrinSamun Nasara:
Yana daga cikin abubuwa mafiya muhimmanci da suke isar da mutum zuwa ga cimma burinsa shi ne: Jajircewa a aiki.
Idan ka lura da abin da ke gudana a tsakanin halittu da abin da ke gudana tare da su, za ka fahimci wata hakika ta cewa dukkan wani samamme yana bayyanar da samuwarsa, ta hanyar gariza ko fidra, cewa samuwarsa da cikar halittarsa yana da alaka da iyaka kokarinsa ko fadi-tashinsa.
Azahiri wannan fadiwar da wasu suke yi wasu kuma suke tashi, yana yin nuni ne ga wannan hakika ta yinkurin da kowanne sammae yake yi. Hakika Allah madaukakin sarki ya halicci mutum a wannan rayuwar ne domin ya yi aiki ya samar da ci-gaba, kuma babu bambanci a tsakanin namiji da mace a wannan.
Allah madaukakin sarki yana fada a cikin suratun Nahl: 97:
(مَنْ عَمِلَ صَالِحًا مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَى وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَنُحْيِيَنَّهُ حَيَاةً طَيِّبَةً وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَجْرَهُم بِأَحْسَنِ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ).
Ma’ana: Duk wanda ya yi aiki na kwarai namiji yake ko mace, yana mai imani, to za mu rayar da shi rayuwa mai kyau, kuma mu saka musu da mafi kyawun dabin da suke aikatawa.
Lallai malamai da sauran manyan mutane maza da mata, ba su kai ga wadannan matsayai da suke a kansa na nasara ba sai da jajircewar aiki.
Wanda kuwa yake ganin zai iya cimma burinsa yana zaune ba tare da yin aiki ba ya yi kuskure. Allah madaukakin sarki yana fada a cikin suratun Najmi:39-42:
(وَأَن لَّيْسَ لِلْإِنسَانِ إِلَّا مَا سَعَى *وَأَنَّ سَعْيَهُ سَوْفَ يُرَى * ثُمَّ يُجْزَاهُ الْجَزَاء الْأَوْفَى * وَأَنَّ إِلَى رَبِّكَ الْمُنتَهَى).
Ma’ana: Ba za ba wa mutum ladan wani abu ba sai abin da ya yi sa’ayi a ranar lahira, kuma za a nuna masa ladan sa’ayin nasa, za kuma a yi masa cikakken hisabi, kuma zuwa ubangijinka za a koma.
Tabbas rayuwa tana nuna cewa mutum ba zai isa ga hadafinsa madaukaki ba sai da aiki tukuru.
Akwai kyakkyawar alaka tsakanin ci gaba da kuma yin aiki, mutumin da ya jajirce yana ci gaba ne gwargwadon fafutukarsa, haka nan al’ummar da ta ci gaba a wayewa tana amfana da son yin aiki, da aiki tukuru ne take bambanta da watanta.
Masu hikima suna cewa: Mutane iri uku ne: Mutumin da yake fafutuka, da wanda yake kokwanto, da kuma wanda ya debe haso. Mutum na farko: Yana yin nasara a kowane abu. Mutum na biyu kuma: Ba ya iya cika komai. Mutum na uku kuwa: A kowane abu sai ya yi asara.
Masu magana suna cewa: Jajirtacce shaidani ne kadai yake yaudararsa; Shi kuwa mai kasala kowa ma yaudararsa yake yi.
MENE NE FA’IDAR YIN AIKI?
Yin aiki yana da fa’idoji masu yawa:
1 – Biyan bukatar kai tare da samun lafiyar jiki, mutumin da yake yin aiki yana jin cewa yana yin aikin da yake gabansa ne, a matsayinsa na daya daga cikin al’umma, kuma a matsayinsa na lafiyayyen mutum.
Lamarin sabanin haka yake ga mutanen da ba sa yin aikin komai domin cimma manufarsu, ire-iren wadannan suna fuskantar damuwa tare da kuncin zuciya, na daga asara da yanke kauna, kuma sun fi kusa da kamuwa da cututtuka na tunani da na jiki.
2 – Yin aiki garkuwa ne daga baci, yana daga cikin abin da yake lalata mutum: Kasala da lalaci. An ce: Jinkiri yana haifar da bacin rai, lalaci kuma yana haifar da talauci da halaka, duk wanda bai nema ba ba zai samu ba.
3 – Aiki shi ne sirrin ci gaba, kuma dama ce ta samu, sannan shi ne yake kai al’umma da daidaikunta ga ci gaba. Kasala da son hutu suna daga cikin abin da ke hana mutum ci gaba.
Don haka yana da matukar muhimmanci ga kowannenmu ya tashi ya yi aiki gwargwadon ikonsa, domin al’umma ta rayu cikin dauwamammen nishadi tare da fitar da ‘intaji’ na har abada, sai ya kasance mun shiga cikin al’ummun da suka ci gaba. duk al’ummar da ta kasance ba ta intaji sai sarrafarwa to ba za ta taba ci gaba ba.
Da yin aiki ne mutum yake isa ga manufarsa, da aiki ne ake raya kasa, da shi zukata suke nutsuwa, da kuma shi ne ake tara wani abu, da shi ake samun daukaka, da shi ake warware matsaloli, ke nan aiki shi ne abu guda daya da yake tafiyar da dukkan rayuwa, ake gina dukkan hanyoyin duniya da na lahira.
SHARADAN CI GABA DA AIKI:
1 – Ikhlasi, wato kyautata aiki:
Yana daga abu mafi muhimmanci wajen karbar aiki a wurin Allah ta’ala: Kyautata aiki, wato nufin Allah ta’ala da aiki tare da tsarkake shi daga dukkan komai. Lallai ne mai yin aiki ya kasance yana da kyakkyawar manufa, kada ya raba wani abu a wurin gudanar da aikin nasa wanda ba shi ne hadafinsa na farko ba, da wannan ne kyautata aiki yake tabbata ga Allah ba ga waninsa ba. Ya tsarkake kansa daga wasu manufofi kamar riya son a sani, ko son a yabe shi, ko don ya samu kudi da wanin wadannan.
2 – Lura Da Kyawun Aiki Ba Yawansa ba: Kyawun aiki yana da alaka da yadda aka yi ba yawan aikin ba, aiki ingantacce da aka yi shi da kyakkyawar niyya kuma aka yi shi da takawa shi ne yake da kima komai kankantarsa, aikin kuwa da babu kwarewa da ikhlasi a cikinsa, aka cakuda shi da riya da son a sani, ba shi da kimar koma, komi yawansa, saboda haka Allah madaukakin sarki yake cewa: (أيكم أحسن عملا) wato wanda ya fi kyautatata aiki a cikinku, bai ce: Wanda ya fi yawan aiki a cikinku ba. Abin da yake ba wa aiki kima shi ne kyautatawa tare da yinsa yadda ya kamata.
3 – Dorewa: Sanannen abu ne cewa kowane aiki aka daukansa a matsayin mai tasiri ko bayar da kyakkyawan sakamako ne idan ya kasnace mai ci gaba, aikin da ake yinsa a tsintsinke ba ya ba da wata fa’ida ta a zo a gani, kuma yana da kashe jiki, domin barin aiki yana kashe jiki, kamar yadda ci gabansa yake bayar da nishadi da karsashi.
Wani lokacin fara aiki yana zama mai sauki, sai dai ci gaba da yinsa yana zama mai wahala, kuma ana samun kyakkyawan sakamako ne a cikin jajircewa wajen yin aiki.
4 – Gabatar da abu mafi muhimmanci a kan abu mai muhimmanci. Imam Ali (a.s) yana cewa: Duk wanda ya shagaltu da yin abu mara muhimmanci to zai bar abin da ya fi muhimmanci.
Ana kiran wannan ka’ida da: Ka’idar muhimmi da wanda ya fi muhimmanci, domin ayyuka a wannan rayuwar ba daraja daya suke da ita ba wajen muhimmanci, akwai ayyukan da suka zama na dole da wadanda ba na dole ba. Sai dai da yawan mutane sun fi mayar da hankali a kan abin da bai zame musu wajibi ko dole ba, su bar abin da ya zama na wajibi a kansu, misalan haka suna da yawa.
5 – Yin aiki a cikin jama’a: Yin aiki iri biyu ne:
– Aikin daidaiku.
– Aikin jama’a.
Na farko yana nufin mutum ya yi aiki shi kadai, aikin nasa ne ko na al’umma.
Na biyu kuma yana nufin: Hada hanun wasu jama’a domin yin aiki tare, wannan abin na kasuwanci ne ko kungiya, su yi taimakekeniya, wato gudanuwar aikin ya kasance na jama’a.
Aikin jama’a yana da fa’idoji masu yawa, kuma ya fi bayar da kyakkyawan sakamako fiye da na mutum shi kadai.
– Aikin mutum daya yana tsayawa yayin faruwar wani abu mara kyau, shi kuwa aikin gamayya ba ya tsayawa sakamakon rashin mutum guda daga cikinsu, aikin zai ci gaba ko da babu shi.
– Aikin gamayya ba ya cin lokaci kamar na mutum shi kadai, kuma ya fi bayar da natija mai yawa.
Yin taimakekeniya domin isar da sakon Musulunci ga duniya baki daya ta hanyar mu’assasosi da yada makaloli litattafai da samar da kafofi na sadarwa lamari ne mai girma a Musulunci. Allah madaukakin sarki yana fada a cikin suratul Ma’ida: 2:
(وَتَعَاوَنُواْ عَلَى الْبرِّ وَالتَّقْوَى).
Ma’ana: Ku yi taimakekeniya wajen aikin da’a.
Wannan yana jan halkalin mutane ne wajen hada hannu domin yin da’a ga Allah a kowane hali a kuma kowane zamani a kuma kowane wuri, kada Shedan ya yaudare su wajen kawar da su ga bin hanyar Allah ta’ala. Sai ayar ta ci gaba da cewa:
(وَلاَ تَعَاوَنُواْ عَلَى الإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ).
Ma’ana: Kada ku yi taimakekeniya wajen aikata sabo da yin ta’addanci.
© Mujtaba Shu’aibu Adamu