September 3, 2023

SIRRIN SAMUN NASARA MATAKI NA HUDU: DAMA TA YALWAR LOKACI

DAMA TA YALWAR LOKACI

Ka ribaci lokacinka kafin shagaltuwarka. Lallai dama ta yalwar lokaci ba kowa ne ya fahimce ta ba, sai ‘yan kadan daga cikin mutane, da yawa suna da yalwar lokacin da ya ishe su su yi ayyuka masu yawa, amma ba su amfana da shi ba, sai su bar abin sai nan gaba za su yi, su shagaltu ga barin aikin da za su iya yinsa a yanzu, a tsammaninsu nan gaba za su yi shi, da wannan zaton nasu sai su yi asarar yanzun, kuma ba su riski nan gaban ba.
Lallai batu game da lamarin bata lokaci abu ne da ya mamaye al’ummarmu ta musulmai, da a ce kowa zai yi wa kansa kididdiga na lokacinsa, da ya samu cewa tazarar da yake batawa a rayuwarsa tana da yawa.
Imam Aliyu (a.s) yana cewa: “ (Ku yi aiki) Yanazu yanzun nan kafin ku yi nadama, tun kafin rai ya ce: Kaicona! Ina ma ban yi sakaci wajen bin umarnin Allah ba, da ban kasance cikin masu yi wa manzo da muminai izgili ba. Ko kuma ta ce: Da Allah ya shirye ni da na kasance cikin masu tsoronsa. Ko kuma lokacin da ya ga azaba ya ce: Ina ma za a mayar da ni duniya da na kasance cikin masu kyautata aiki.

DAMA A RAYUWA
Ka ribaci rayuwarka kafin mutuwarka:
Rayuwar mutum dakkaninta dama ce, domin mutum ba ya dauwama a wannan rayuwar, ya so ko ya ki, dole sai ya mutu a wata rana.
Don haka kada ku jinkirta aikin da za ku yi shi a yau ya kai gobe, kullum ku rinka tuna cewa kwanakinku karewa suke yi kuna kusantar ajali, ku yi kokarin yin aiki domin ku samu nasara, ku samu nishadi ta hanyar ribatar lokacinku.
Wata rana an tambayi Abumuslim Alkhurasani cewa: Mene ne sirrin samun nasararka?
Sai ya ce: Ban taba barin aikin da zan yi shi a yau ba, in kai shi gobe.
Lallai mutum yana da damarmaki masu yawa tare da yawaitar abubuwan da zai amfana da su baja-baja, to mene ne yake hana ci gaba da tafiya zuwa ga samar da rayuwa mai dorewa?
Yana daga cikin abin da yake yi wa mutum dabaibayi: Rashin fadaka ko yin rige-rige wajen aikata alheri.
Allah madaukakin sarki yana fada a cikin suratul Hadid 21: Ku yi rige-rige wajen neman gafarar ubangijinku…
Mutum mai nasara shi ne wanda yake kalubalantar aubuwan da suke hana shi isa ga aikata alheri, yin gaggawa zuwa ga aikata kyawawan ayyuka.
Mawaki yana cewa:
– Numfashin rayuwarka kudin sayen aljanna ne, kada ka sayi harshen wuta da shi a ranar tashin alkiyama.
– Ya kai mai bata da rayuwarsa ga sabon mahaliccinsa, ka farka daga mayen giyar son rai da kake yi.
Sarkin muminai Ali (a.s) yana cewa: “Lallai dare da rana aiki suke yi a kanka, kai ma ka yi aiki a kansu, kuma suna karba daga gare ka, kai ma ka karba daga gare su”.
Ya sake cewa: “Me ya fi lokaci sauri a cikin rana, ya fi saurin raneku a cikin wata, ya fi watanni sauri a cikin shekara, ya fi shekaru sauri a cikin rayuwa”. Nahjulbalaga, Khudba: 188.
Ya kara da cewa: “Yanzu yanzun nan! Matsawar kana da dama, fitila a kunne take, kofar tuba a bude take, tun kafin alkalami ya bushe, a nade takardu”.
Lallai bata lokaci da yin watsi da dama alama ce ta asararrun mutane a rayuwa, a daya gefen kuma yin amfan da lokaci da ribatar dama alama ce ta wadanda suka yi nasara a tsawon tarihi.
Allama majlisi ya rubuta wani sashi na: Biharul Anwar a lokacin da yake tafiya a kan rakumi yayin tafiye-tafiyensa.
Haka kuma Shahidul Auwal Jamaluddin Al’amuli (Allah ya gafarta masa), ya rubuta risalarta da ake kira da: Lum’a Dimashkiyya, a lokacin da yake tsare a kurkuku, duk da wahalhalu da azabtarwa na kurkuku, an ce ma hukuncin kisa aka yanke masa. Don haka kada ka raina lokaci ka ki yin komai.

© Sheikh  Mujtaba Shu’aibu Adamu.

SHARE:
Makala 0 Replies to “SIRRIN SAMUN NASARA MATAKI NA HUDU: DAMA TA YALWAR LOKACI”