August 26, 2023

Sirrin Samun Nasara. Kashi Na Daya:

GABATARWA
Dukkan yabo ya tabbata ga ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammad tare da iyalan gidansa tsarkaka.
Wata kila zai iya zuwa kwakwalen da yawa daga cikin mata cewa: Mene ne sirrin samun nasara? Kuma ta kaka za mu isa ga cimma burinnmu? Kuma ta ina za mu fara?
Haka kuma, shin zai yiwu ga mace Musulma ta karfafa baiwarta har ta isa ga cimma burinta? Shin Allah ya kebence maza kadai ne wajen samun nasara a rayuwa ban da mata? Ko kuwa Allah ya ba wa maza hankali ne tare da ikon samun nasara a rayuwarsu, ya kuma haramta wa mata?
Domin amsa wadannan tambayoyin zai mu ce: Lallai sirrin samun nasara tare da ci gaban dan Adam namiji ne ko kuwa mace yana tattare da samuwarsa da wadatuwarsa da kuma matakan da yake dauka game da makomarsa. Babu wanda zai samu nasara sai wanda ya lissafa kansa cikin masu kokarin tabbatar da manufarsu. Kyakkyawan shiri ga kai shi ne matakin na farko wajen tunkarar hadafi madaukaki.
Imam Ali (a.s) yana fada a cikin Nahjul Balaga, hikma ta 149:
(هلك امرؤ لم يعرف قدره).
Ma’ana: mutumin da bai san kimarsa ba ya halaka.
Dmin kuwa mutumin da ya jahilci kansa, ko ya jDA Allah ya yi maka, mataki ne muhimmi wajen fuskantar mafi girman nasara.
Imamu Ali (a.s) yana fada a cikin littafin: Diwanin imamu Ali: 175:
وتحسب أنك جرم صغير وفيك انطوى العالم الأكبر
Ma’ana: Kana ganin kanka a karamar halitta idan aka kwatanta ka da mafi yawan halittu, alhali a tare da kai sirri da girma yake tajalli.
Idan muka bibiyi rayuwar malamai da wasu manyan mutane za mu same su mtuane ne na al’ada kamar kowa, sai dai sirrin samun nasararsu ita ce: Sun fahimci baiwarsu sai suka amfana da ita ta hanyar yin kokari yin aiki da tunani har suka zamo abin da suka zama.
Don haka ke ma za ki iya shiga sahu, ki rubuta sunanki cikin rukunin manya. Ana cewa: A bayan kowane babba akwai mace mai girma, kuma mace ita ce sirrin girman namiji.
Don haka kada ki ce ba zan iya ba, ko wannan abin ya fi karfina, ko wannan abin ba zai yiwu ba, Ki sa wa ranki cewa zai yiwu. Daya daga cikin malaman Falsafa yana cewa: Babu abin da ba zai yiwu ba, duk abin da waninka zai iya shi, to kai ma za ka iya.
Napoleon yana ba da amsar abubuwa uku da abu uku:
– Wanda ya ce: Ba zan iya ba, sai a ce da shi: Ka kokarta.
– Wanda kuwa ya ce: Ban sani ba, sai a ce da shi: Ka koya.
– Wanda kuma ya ce: Ba zai yiwu ba, sai a ce da shi: Ka jarraba.
Abin da yake a gabanki a mataki na farko shi ne: Ki fahimci baiwarki, ki jarraba ta, ki amfana baiwar da take boye tare ke, a nan ne za ki ga darajarki tana daukaka zuwa ga cikar samun nasara.
Lallai ne mu yi nuni da cewa: Zai yiwu lamarin ya yi miki wahala a mataki na farko, kuma yana da kyau ki san cewa, farkon kowane lamari yana da wahala a matakin farko, sai dai a karshe za ki ga amfanin da zai bayyana, da sharadin lallai sai kin jajirce kin tunkari kalubalen da hakuri, ki yi tsayin daka, ki cire debe haso da jin karaya.
Kada ki ji tsoron faduwa, domin ita hanya ce da cin nasara, ba a samun nasara sai da fadi-tashi, tare da daukan izina ga wanda ya kayar da kai. Dukkan wadanda kike ganinsu manya sun sha fadi-tashi kafin su zama abin da kike ganinsa a matsayin girma, sun dauki darusa tare da izina domin hankoron abin da suke son cimma a wata rana.
Saboda haka, wannan littafin zai yi bayanin wasu matakai na isa ga matsayai na daukaka a kowane bangare na rayuwa. Za mu yi nuni ga wasu ka’idoji a takaice wadanda ba su takaita da wasu mutane daban ba, za su amfani kowa maza da mata, muna dogaro ga Allah, shi ne abin dogaro.

Daga:Maman Musdafa
✍🏽 Wanda ya fassara:
Mujtaba Shu’aibu Adamu

SHARE:
Makala 0 Replies to “Sirrin Samun Nasara. Kashi Na Daya:”