June 5, 2023

Siriya : ‘Yan Adawa Sun Bukaci Komawa Tattaunawa Da Gwamnati.

‘Yan adawa a Siriya, sun bukaci komawa tattaunawa da gwamnatin Shugaba Bashar Al-Assad a shiga tsakanin MDD.

A sanarwar da kwamitin da ya kunshi ‘yan adawa na siriya ya fitar ya ce, abubuwa dake faruwa a matakin kasa da kasa da yankin, da kuma halin da ake ciki a Siriya, sun bada tabbaci na yadda za’a komawa tattaunawa ta kai tsaye.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kasashen larabawa ta dawo da Siriya mamba a cikinta, sai kuma yadda wasu kasashen larabawa suak dawo da alaka da Siriyar a baya baya nan.

Saidai ‘yan adawan na Siriya sun ce dawo da Siriya a fagen siyasar kasashen larabawan, na da hadarin gwamnatin kasar ta yi watsi da duk wani yunkuri na lalubo hanyoyin magance rikicin kasar ta hanyar siyasa.

A wani jawabi a gaban kwamitin tsaron MDD, a kasrhen watan Mayu, wakilin musamman na MDD, kan rikicin Siriya, Geir Pedersen, ya bayyana cewa dawowar da Siriya a fagen diflomatsiyya a yankin, dama ce da ya kamata a yi amfani da ita idan ta samu.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Siriya : ‘Yan Adawa Sun Bukaci Komawa Tattaunawa Da Gwamnati.”