October 21, 2021

Siriya: Shugaban Asad Ya Zanta Da Mohammad Bin Za’id Yeriman Abuzabi

Daga shafin Hausatv


Shugaban kasar Siriya Bashar Al-Asad ya zanta ta wayar tarho da yerimai mai jiran gadon sarautar Abuzabi a jiya Laraba.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin labaran kasar Siriya SANA ya na cewa bangarorin biyu sun tattauna al-amura da suka shafi kasashen biyu, daga ciki har da batun huldan tattalin arziki da kuma al-amuran siyasa tsakanin kasashen biyu da kuma na yankin gabas ta tsakiya.

Labarin ya kara da cewa bayan zantawa tsakanin shuwagabannin biyu, shugaba Al-Asad ya bukaci a kafa kwamitin tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Har’ila yau yerima Mohammabin bin Za’id Aali Nahyaan ya bukaci aiki tare da kasar Siriya a dukkan bangarori tattalin arziki da kuma shirin sake gina kasar Siriya bayan an kawo karshen yakin cikin gida a kasar.

Kafin haka dai ministan harkokin wajen hadaddiyar daular larabawa (UAE) Abdullahi bin Zaid Aali Nahyaan ya bada sanarwa a cikin watan Maris da ya gabata kan cewa komawar kasar Siriya kan kujerarta a kungiyar kasashen larabawa ya zama dole.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Siriya: Shugaban Asad Ya Zanta Da Mohammad Bin Za’id Yeriman Abuzabi”