Siriya: Jiragen Yakin Rasha Sun Yi Luguden Wuta A Kan Sansanin Yan Ta’adda “Hai’atu Tahriri Sham.

Jiragen yakin kasar Rasha a Siriya sun yi luguden wuta kan sansanin mayakan kungiyar yan ta’adda ta “Hai’atu Tahriril Sham’ mai biyayya ga babban kungiyar yan ta’adda ta ‘Jbahatun Nusra’ a yamma garin Idlib kusa da kan iyakamda kasar Turkiya.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto wani babban jami’an tsaro na sojojin Rasha a kasar ta Siriya yana cewa da farko jiragen yakin leken asiri na kasar ta Rasha sun yi shawagi a yankin a kuma kan sansanin inda suka ga yadda yan ta’adda suka kai kawo da wasu kayaki a wani wuri a yankin, wanda kuma ake zaton jiragen yaki ne wadanda ake sarrafasu daga nesa, kuma mai yuwa suna shirin kai hare-haren ta’addanci a cikin kasar ta Siriya ne.
Labarin ya kara da cewa jiragen yakin kasar Rasha bayan tattara isassun bayanai ta yi luguden wuta a kan sannanin mayakan da ke garin Sarmada cikin lardin Idlib kuma kusa da kan iyaka da kasar Turkiya, inda bayan lalata rumbun makaman yan ta’adda akkalla 6 daga cikinsu sun halaka.
Kungiyoyin yan ta’addan wadanda suke mamaye da wasu yankunan a lardin Idlib tare da taimakon kasashen yamma suna samun makamai da kuma jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa wajen kai hare-hare cikin cikin.
©voh