April 1, 2024

ShugabaTinubu ya kafa wata kungiya domin lalubo hanyoyin magance matsalar tattalin arziki

 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kafa wata kungiya mai zaman kanta da za ta samar da hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar tattalin arzikin kasar.

Farashin kayan abinci da man fetur sun yi tashin gwauron zabo amma da dama na kokawa saboda yadda albashin su bai bi sauye-sauyen ba.

Matsalolin tattalin arziki sun haifar da wahalhalu da kuma matsin lamba ga gwamnatin Tinubu.

Shugaban ya umurci tawagar da ta gabatar da wani cikakken shiri na tunkarar tattalin arziki cikin makonni biyu, wanda daga nan za a fara aiwatar da shi cikin watanni shida masu zuwa.

Rundunar ta ƙunshi manyan jami’an gwamnati da shugabannin masana’antu.

Shugaban ya kuma kafa kwamitin kula da harkokin tattalin arziki na shugaban kasa (PECC) – wacce shi ne zai jagoranta – don sa ido kan sauye-sauyen tattalin arziki.

#Najeriya

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “ShugabaTinubu ya kafa wata kungiya domin lalubo hanyoyin magance matsalar tattalin arziki”