April 17, 2023

Shugabannin kasashen Chadi da Najeriya sun gana a kasar Saudiya kan rikicin siyasar kasar Sudan.

A ranar lahadi 16 ga wata shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na kasar Chadi Mahamat Idris Derby suka yi kiran da a gaggauta kawo karshen rikicin da ya  barke tsakanin dakarun sojin kasar Sudan da mayakan rundunar kai daukin gaggawa don tallafawa ayyukan tsaro ta RSF.

Shugabannin biyu sun bukaci hakan ne a birnin Macca yayin wata ganawa da suka yi.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da karin bayani

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun hadimin shugaban Najeriya kan sha’anin yada labarai Garba Shehu ta yi bayanin cewa shugabannin kasashen na Najeriya da kuma na Chadi sun nuna rashin jin dadinsu kan rikicin da ya barke tsakanin dakarun tsaron kasar ta Sudan.

Sun ce muddin dai za a rinka samun sabanin ra’ayi a tsakanin mutanen da aka dorawa alhakin tabbatar da tsaro a kowacce kasa to kuwa al’ummar kasar za su ci gaba da kasancewa ne cikin yanayin rayuwa mara tabbas ta fuskar zaman lafiya.

Shugabannin kasashen biyu dai sun ce yanzu haka abin dake faruwa a wasu daga cikin biranen kasar ta Sudan ciki har da babban birnin kasar ya tayar da kungiyar tarayyar Afrika da kuma sauran kasashen duniya tsaye, a cewar su rikicin babban barazana ne ga fafutukar samar da dauwamammen zaman lafiya a kasashen da yankin Afrika ta tsakiya.

Yayin tattaunawar dai kamar yadda sanarwar ta bayyana, shugaban gwamnatin rikon kwaryar Chadi Mahamat idris Derby ya shaidawa shugaba Buhari cewa tuni ya bayar da umarnin rufe dukkan iyakokin da suka hade kasar Chadi da Sudan, tare kuma da kara tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin.

Yayin da shi kuma shugaba Buhari ya tabbatar da cewa ya samu damar magana da jagororin bangarorin da suke rikici da juna, inda ya nemi kowa a cikinsu ya ajaye makaminsa domin samun damar hawan teburin sulhu.

Haka kuma sanarwar ta ambato shugaba Buhari na kira ga sauran kasashen makwafta da kuma sauran kasashen duniya da su yi kokari na ganin cewa an samu fahimtar juna tsakanin sojojin kasar da kuma dakarun sa kai na RSF.

Ya ce hakika halin da kasar ta Sudan ke ciki yanzu abin takaici ne mutuka, ganin yadda rayukan fararen hula ke ci gaba da salwanta.

Daga bisani shugaba Buhari ya yaba da kokarin shugaban rikon kwaryar kasar ta Chadi wajen ganin yadda ya dawo da zaman lafiya a kasar tasa, inda ya kara bukatarsa da ya kara jajircewa sosai.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Shugabannin kasashen Chadi da Najeriya sun gana a kasar Saudiya kan rikicin siyasar kasar Sudan.”