Shugaban Tarayyyar Afirka Zai Kai Ziyara Birnin Khartum Na Kasar Sudan.

Shugaban kungiyar tarayyar Afirkan,Musa Faki Muhammad zai kai ziyarar gaggawa zuwa kasar Sudan domin samo hanyar tsagaita wutar yaki.
A jiya Lahadi ne kungiyar tarayyar Afirkan ta sanar da cewa shugaban nata zai ziyarci kasar Sudan wacce fada ya barke a cikinta a tsakanin bangarori biyu na sojoji da kuma rundundar kai daukin gaggawa.
Sanarwar da kungiyar ta tarayyar Afirkan ta fitar ta kunshi yin kira ga bangarorin biyu dake fada da juna da su tabbatar da cewa sun kare fararen hula.
Wannan sanarwar dai ta fito ne bayan wani taron gaggawa na kwamitin sulhu da zaman lafiya na kungiyar da ranar jiya Lahadi a birnin Addis Ababa.
Kwamitin sulhu da zaman lafiyar na kungiyar ta Afirka ya yi kira ga shugabanta da ya yi amfani da ofishinsa domin ganin bangarorin biyu da suke fada da juna sun tsagaita wuta.
A yau Litinin fadan da ake yi a Sudan din ya shiga kwana na uku,inda a jiya aka sanar da kashe fararen hula 56 a cikin sa’oi 24 daga barkewar yakin. MDD ta ce da akwai ma’aikatanta uku a tsakanin wadanda aka kashe.