January 27, 2024

Shugaban masu gwagwarmaya a majalisar dokokin kasar Lebanon ya gargadi Israila

 

Shugaban kwamitin masu wakiltar gwagwarmaya a majalisar dokokin kasar Lebanon Muhammad Ra’ad ya gargadi HKI akan gigin bude yaki gadan-gadan da kasarsa yana mai kara da cewa; “Mun gina wa Isra’ila kabarurruka.”

Muhammad Ra’ad ya cigaba da cewa; Mun shirya tsaf domin kwafsa yaki fiye da yadda abokan gaba suke zato, kuma a halin yanzu abinda abokan gaba su ka gani wani yanki ne kadan na karfinmu, to mun shirya domin nuna masa hakikanin karfin da muke da shi.”

Shugaban kwamitin ‘yan majalisa masu wakiltar gwagwarmaya a Lebanon wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron girmama daya daga cikin shahidan gwgawarmayar a garin Nabadhiyyah, ya ce; “ Abinda muke yi a yanzu saboda Gaza kare manufofin ne na kasa, kuma taimaka wa wadanda ake zalunta ne, domin babu yadda za a bar Gaza ita kadai ana kai mata hare-haren ta’addanci da nuna wariya irin na ‘yan sahayoniya.”

Da yake Magana akan goyon bayan da Amurka take bai wa HKI, Muhammad Ra’ad ya ce “Amurka tana bata lokaci ne kawai domin Isra’ila tana gangarar cin kasa ne, ba Amurka ko waninta da zai iya sa waigin da zai dakatar da ita.

 

©Hausa tv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Shugaban masu gwagwarmaya a majalisar dokokin kasar Lebanon ya gargadi Israila”