April 28, 2023

Shugaban Kasar Turkiya Yace Kasarsa Ta Shiga Cikin Jerin Kasashe Masu Fasahar Nukliya A Duniya

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Urdugan yana fadar haka a jawabinda shi da kuma shugaban Vladimir Putin suka gabatar ta hotunan bidiyo a jiya a bikin bude ciyar.

Urdugan ya kara da cewa cibiyar samar da wutan lantarki tare da amfani da makamshin Nukliya ta ‘Ukkuyu’ aiki ne na hadin giwa na farko tsakanin kamfanonin cikin gida na kasar Turkiya tare da hadin kai da kamfanin Rosatom na kasar Rasha. Kuma an kashe mata dalar Amurka billion 20, sannan ana saran cibiyar zata samar da wutan lantarki mai karfi megawats 4,800, sannan zai kai kuryar karfinsa a shekara ta 2028.

An fara aikinta a shekara ta 2018 sannan a halin yanzu kasar na shirin gina sabbin cibiyoyi guda biyu a yankuna daban-daban na kasar. Girgizaman kasa na watan fabrairun da ya gabata dai bai shafi cibiyarba wanda ya nuna ingancin aikinsa.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Shugaban Kasar Turkiya Yace Kasarsa Ta Shiga Cikin Jerin Kasashe Masu Fasahar Nukliya A Duniya”