April 5, 2023

Shugaban kasar Faransa ya isa birnin Beijing

Shugaban kasar Faransa ya isa birnin Beijing
Da yammacin Larabar nan ce, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, don fara ziyarar aiki daga 5 zuwa 7 ga wata bisa ziyarar takwaransa na kasar Xi Jinping.
Wannan shi ne karo na uku da Macron ya kawo ziyara kasar Sin bayan hawansa karagar mulki a matsayin shugaban kasar Faransa, kuma ziyararsa ta farko a kasar Sin a wa’adinsa na biyu na shugabancin kasar.

© (Amina Xu)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Shugaban kasar Faransa ya isa birnin Beijing”